20/02/2026
GIDAUNIYAR RAMADAN 2026/1447
Da farko muna masu miƙa godiyar mu ga Allah S.W.T da ya Ƙaddare mu da riskuwar wannan watan mai alfarma kuma ya bamu ikon fara gudanar da wannan aiki cikin nasara.
Bayan haka muna miƙa godiya ga ɗaukacin Excos na wannan gidauniya, membobin ta da dukkan al'ummar musulmi da s**a bada gudummawar su wajen ganin an fara gudanar wannan aikin alkharin, Allah S.W.T ya sakawa kowannen mu da mafificin alkhairi, Allah ya ƙarbi ibadun mu ya ƙara mana buɗi acikin harkokin mu.
A taƙaice wannan shine yadda aka gudanar da rabon kayan abinci da da kayan sallah (sutura) domin watan Ramadan da kuma bukukuwan sallah, Sauran ayyukan gidauniyar kuma suna gudana in shaa Allah, kamar rabon ƙanƙarar ruwa da kuma aikin naman sallah (Tonton) da muke fatar a gudanar da gudummawar da kuke bayarwa, muna fatan zaku cigaba da bada gudummawar ku wajen tallafawa waɗannan marayu.
Allah ya saka maku da alkhairi.