Muri Social Connect

Muri Social Connect Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Muri Social Connect, Nonprofit Organization, Jalingo.

Haɗin kai da aka nuna a yayin wannan tattaunawa ya nuna alamar sabuwar rayuwa ga ƙungiyar MURI Social Connect, inda mamb...
13/07/2026

Haɗin kai da aka nuna a yayin wannan tattaunawa ya nuna alamar sabuwar rayuwa ga ƙungiyar MURI Social Connect, inda mambobi s**a bayyana aniyarsu ta sake farfaɗo da ƙungiyar tare da ƙarfafa zumunci, haɗin kai da kuma haɗa kan 'ya'yan Muri domin ci gaban juna.

Mahalarta taron sun jaddada cewa lokaci ya yi da za a sake gina ƙungiyar bisa turbar gaskiya, riƙon amana da aiki tare, domin ta zama wata kafa da za ta haɗa 'ya'yan Muri a gida da waje, tare da samar da damar bunƙasa tattalin arziki, ilimi, ci gaban matasa, taimakon juna da kuma amfani da fasahar zamani wajen sadarwa da aiwatar da shirye-shiryen ci gaba.

An kuma bayyana fatan cewa sabon salon jagoranci da haɗin kan da aka nuna zai ba ƙungiyar damar sake samun karɓuwa a tsakanin mambobi da sauran al'umma, tare da mayar da ita wata ƙungiya abin koyi wajen gudanar da ayyukan ci gaba da walwalar jama'a.

Da yake bayyana ra'ayinsa, ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar, Usama Muhammad Bello, ya ce akwai buƙatar dukkan mambobi su ajiye bambance-bambance a gefe, su rungumi haɗin kai domin cimma manufofin da aka kafa ƙungiyar a kai.

Ya ce:

"Lokaci ya yi da za mu dawo mu haɗu a matsayin dangi guda. MURI Social Connect ta wuce ta zama ƙungiya kawai; gida ce da ta haɗa mu. Ya zama wajibi mu yi amfani da damarmu, ƙwarewarmu da kuma fasahar zamani wajen tallafa wa juna, bunƙasa rayuwar mambobi da kuma bayar da gudunmawa ga ci gaban Muri da Jihar Taraba baki ɗaya. Idan muka haɗa kai, babu abin da ba za mu iya cimma ba."

A ƙarshe, mambobin sun yi kira ga dukkan tsofaffi da sababbin mambobin MURI Social Connect da su mara wa wannan sabon yunƙuri baya, tare da ba da gudunmawar ilimi, lokaci da shawarwari domin tabbatar da cewa ƙungiyar ta zama abar alfahari ga mambobinta da kuma al'umma baki ɗaya.

GWAGWARMAYA DOMIN ALUMMA KARKASHIN KUNGIYAR MURI SOCIAL CONNECT 💪❤️💚Fuskoki, ko kace idanuwa masu haske na jakadun Al'um...
07/07/2026

GWAGWARMAYA DOMIN ALUMMA KARKASHIN KUNGIYAR MURI SOCIAL CONNECT 💪❤️💚

Fuskoki, ko kace idanuwa masu haske na jakadun Al'umman yankin muri.

A zahiri matasa sune kashin bayan Al-umma, Amma ba kowadansu irin matasa ba wasu matasan cutar da Al'umma suke.

Hanya mafi sauki kowadansu Irin Al'umma sunada irin tasu Gudumawa da sukegani zasu iya bayarwa domin ganin Ansamu cigaba, da Kawo sauyi a lokacinda Al'umma suke tsananin bukatar sauyi.

Munyi dace da shawarwari MUKA SAMARDA KUNGIYA MAI ZAMAN KANTA A GOMNATANCE MAI SUNA MURI SOCIAL CONNECT ❤️

Wannan dama da muka samu yabamu daman gudanarda Ayyukanmu da manufofinmu daidai da martabar Muri, dakuma Alkawarin kareta da martabarta a duk inda muka tsinci kawunanku.

Muhimman Aiyyuka da suke gabanmu a yanzu👇

1. Hidiman marayu

2. Zamanantar da harkokin Almajirai ta yadda zasuje suyi karatun Allonsu sannan sudawo suje makarantan Boko.

3. Ayyukan jinkai, dakuma wayarda kai idan duk wani Annoba ta taso ko ibtila'i.

4. Farfado da Al'adun gargajiya, tareda taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya cikin Al'umma.

5. Zakulo hazikan matasa wadanda suke bayarda gudumawa, dakuma sadaukar da Rayuwansu domin Al'umma, ta hanyar karfafa musu guiwa dakuma basu Lambar yabo.

NASAN ZAKU IYA TAMBAYA
ina Wannan kungiyar take samun kudi domin gudanarda Ayyukanta?

Magana ta gaskiya tun farkon tashi Wannan kungiyar, tayi iya kokarinta wajen tuntuban matasa maza da Mata masu sana'a domin ayi Wannan tafiya dasu.

Kuma anyi dace Duk cikin tafiyar Ansamu masu dogaro dakansu, walau Dan kasuwa ko Mai sana'ar hannu, ko kuwa ma'aikacin gomnati ko kamfani.

Duk lokacinda bukata ya tashi na wani Aiki ajikinsu suke cirewa ayi hidimar har karshe.

ANSHA TAMBAYA

ko akwai wani Dan siyasa dayake daukar nauyinku?

Cikin gida da waje Babu wani Dan siyasa dayake daukar dawainiyar Wannan kungiyar, domin ba kungiyace da aka kafata domin yiwa wani Aikiba.

Amma akwai inda kungiyar zata iya gogayya da Yan siyasa.

MISALI
Akwai Yan siyasa da suke samar da FOUNDATIONS domin Tallafawa alumma, to anan zakama iya mallakawa kungiyar gudanarda Ayyukanta Baki Daya a madadin ka, domin asamu ingantacciyar daurewar Ayyukan cibiyar.

MISALI NA BIYU
akan samu Yan siyasa da suke bukatan bayarda kayan agaji na gaggawa, sannan suna bukatan Amin tattu domin isar musu da sakonsu Kai tsaye ga wadanda yadace, to nanma kungiyar MSC tana shirye domin hadaka, domin Aikine na jinkai, Yayi dace da manufofinta.

KUNGIYAR MURI SOCIAL CONNECT
tabude kofarta domin karban shawarwari Kai tsaye musamman ta hanun jagoran tafiyar MALAM Shameel isha.

A karshe muna Muku fatan Alkairi, sannan muna bukatar Addu'an Alkairi daga gareku, Allah yabiyamana bukatunmu na Alkairi 🤲

Muri Social Connect
Tuesday, July 7 2026

Address

Jalingo

Telephone

+2348069008641

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muri Social Connect posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share