Arewa Muslim’s Updates

Arewa Muslim’s Updates Trying to tread the path to jannah,remind and inspire the believers in shaa Allah

وفقنا االله جميعا

06/07/2024

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh.

14/06/2024

Sahabbai ‘yan gatan Allah 🥰😍.

Wata rana Manzon Allah (ﷺ) ya ce da Abdullahi Bin Mas’ud (R) “karanta mini Al-Qur’ani in saurara”.
Sai Bin Mas’ud (R) yayi mamaki yace, “Ya Rasulullah! Yanzu kai zan karantawa Al-Qur’ani bayan kai aka saukarwa da shi?”
Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “eh, ina so ne na saurara daga wajen wani ba ni ba”. Sai Bin Mas’ud ya fara karatu daga farkon Suuratun Nisaa’i har yazo kan wannan ayar:

"فَكَيْفَ اِذَا جِئْنَا مِنْ كُلِّ اُمَّةٍۢ بِشَهِيْدٍ وَّجِئْنَا بِكَ عَلٰى هٰٓؤُلَاۤءِ شَهِيْدًا"

(To yaya matsayin mutane zai zama idan muka zo da kowace al’umma tare da mai yi mata shaida, kai kuma (Ya Rasulullah) mu zo da kai kana mai yin shaida kan waɗannan al’ummar?)

Sai Manzon Allah (ﷺ) yace da Bin Mas’ud (R) “ya isa haka”.
Bin Mas’ud (R) yace sai na ɗaga kai na kalli Annabi (ﷺ) sai naga yana hawaye.
Sallallahu alaihi wasallam.

13/06/2024

*🤝BARKANMU DA SAFIYA🤝*
*«NEMAN ILMI»*
"Ilmi Shine Gishrin Rayuwa, Duk Wanda Bashida Ilmi, To Haƙiƙa Yana Cikin Duhu Mai Matuƙar Ban Tsoro, Ka Tashi Ka Nemi Ilmin Addini Dana Rayuwa Sai Allah Ya Sanya Maka Albarka Acikin Rayuwarka"
"Manzon Allah ﷺ, Yace: Duk Wanda Ya Riƙi Wata Hanya Yana Mai Neman Ilimi Acikinta, Allah Zai Sauƙaƙa Masa Hanyar Zuwa Aljannah"

*"Matuƙar Zaka Dage Ka Riƙi Neman Ilimin Addinin Musulunci, To Haƙiƙa Kana Cikin Wata Falala Da Daraja Ta Allah, Zai Sauƙaƙe Maka Hanyar Neman Ilmin Naka, Kuma Zaka Kasance Acikin Wata Kariyar Mala'iku Ta Musamman Har Sai Lokacin Da Ka Dawo Gida"*

31/07/2023

Idan ka lazimci abubuwa guda uku duk hayaniyar duniyar nan Allah zai kare ka (In Sha Allah);
- Cin Halal
- Bin Sumnah
- Yawaita Istigfari

Sheikh Dr Ahmad Bamba (R).

Address

Jalingo

Telephone

+2347068717940

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Muslim’s Updates posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share