Ibrahim Abubakar B Yara

Ibrahim Abubakar B Yara Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Ibrahim Abubakar B Yara, Labor Union, central mosque sabo ibadan, Ibadan.

Tsoho ko uban waye bazamu sake zabar Shiba. Matasa muke so masu Amana. 2027 Nigeria sai matashi mai Amana. InshaAllah
06/08/2024

Tsoho ko uban waye bazamu sake zabar Shiba. Matasa muke so masu Amana. 2027 Nigeria sai matashi mai Amana. InshaAllah

INA KWANKWASO, ABBA GIDA-GIDA SU KA SAMU KURI’UN BOGI GUDA 165,000?Na karanta tsokaci kala-kala tun bayan da kotun tribu...
24/09/2023

INA KWANKWASO, ABBA GIDA-GIDA SU KA SAMU KURI’UN BOGI GUDA 165,000?

Na karanta tsokaci kala-kala tun bayan da kotun tribunal ta ayyana mai girma Dr Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben 18 ga watan maris da ya gabata a Jihar kano.

Amma gabar da mafi akasarin masu irin wadannan sharhi akan shari’ar ke kokarin kubcewa ita ce: wane mahaluki ne ya bawa Kwankwaso da Abba Gida-Gida da Jam’iyyar NNPP zunzurutun kuri’un bogi 165,000 da doriya dan su yi aringizo? Mecece manufarsa? Shin wannan al’adace ta ‘yan kwankwasiyya ko kuma wannan karon su ka fara?

Kamar yadda kotun kararrakin zabe wato Tribunal ta tabbatar wadannan kuri’u babu kwanan wata jikinsu, babu sahannu, haka zalika babu stamp a jikinsu.

Duk wanda ya bibiyi zaben gwamna da aka gabatar a watan maris a wannan jiha zai shaida yadda jikin wakilan Jam’iyyar NNPP s**ai la’asar tun kafin karfe daya na rana, ganin yanda matasa maza da mata s**a dinga kadawa Dr Nasiru Yusuf Gawuna da mataimakinsa Alhaji Murtala Sule Garo kuri’a.

Amma kwatsam sai zaben ya canja bayan an gama kada kuri’u. Wannan dalilin ne yasa Jam’iyyar APC ta fara binkice makasudi, dan tabbas Jam’iyyar ta na da yakinin cin zabenta cikin limana. Daga garshe Allah ya bata sa’a tabankado irin kitimirmirar da Jam’iyyar NNPP da Kwankwaso su ka shirya bayan sun hango faduwa.

Abinda ya faru ya riga da ya faru. Kuma cikin hukuncin ubangiji kotu ta gamsu da korafin Jam’iyyar APC, har ma ta dawowa da Dr Nasiru Yusuf Gawuna kujerarsa a matsayin Halastaccen zababben gwamnan wannan jiha. Shin burin Kwankwasiyya shi ne ta mulki jihar Kano ko ta wane hali?

Amma wani hanzari ba gudu ba al’ummar wannan jiha ta Kano mai albarka tana da hakkin sanin daga ina ne takameme Kwankwaso da Abba Gida-Gida su ka samo wadannan kuri’u na bogi da kuma wanda ya basu.

Ya zama dole Kwankwaso da Abba Gida-Gida su fito su gayawa duniya wanda ya basu wadannan kuri’u na bogi dan su yi aringizo sannan kuma su nemi yafiyar mutanan wannan Jiha..

20/09/2023

Mun sasu fargaba, ciwon Kai, zafin jiki, zazzabi, kuma mukayi nasara akan su. Alhmdllh
GAWUNA has come.

20/09/2023

GAWUNA is around the corner, very soon. Inshallah

18/09/2023

JAHILCIN DA ZAKZAKIY YAKE YADAWA:

1. Jahilci da hayaniyar da Malam Zakzakiy yake yadawa a Duniya a gaban magoya bayansa da sunan bayar da darasi abin takaici ne matuka.

2. Dazun nan ne na yi karo da wani video na shi Zakzakiy yana bayar da darasi a gaban magoya bayansa inda ya soki lafazin “A’ameen” ya ce wai asalinsa maguzanci ne na kafuran Masar! Kuma duk wanda ya furta lafazin bayan karatun Fatiha toh sallarsa ta baci! Ya kuma ce: hatta a littattafan Sunnah ma babu inda aka ce Annabi ne ya ce a rika cewa: “A’ameen” a karshen Fatiha! Haka dai Zakzakiy ya fada babu kunya babu tsoron Allah; duk kuwa da cewa littattafan Sunnah sun ce Annabi ya fadi hakan. Haka nan ruwayah ta inganta a littattafan Shi’ah cewa ana iya fadar hakan!!

3. Na farko dai hadithai da yawan gaske ne cikin littattafan Ahlus Sunnah s**a inganta daga Annabi mai tsira da aminci wadanda a cikinsu Shi Annabi yake umurtan Musulmi da su ce: “A’ameen” bayan fatiha, ga ma daya daga cikinsu a masayin misali: Muslim ya ruwaito hadithi na 404, da Abu Dawud na 972, da Nasa’iy na 655, da Ibnu Khuzaimah na 1,584, da Daramiy na 1,351 daga Sahabi Abu Musal Ash-ary ya ce: خطبنا رسول الله صلى الله عليه وسلم فبين لنا سنتنا وعلمنا صلاتنا فقال: اذا صليتم فاقيموا صفوفكم ثم ليومكم احدكم فاذا كبر فكبروا واذا قال غير المغضوب عليهم ولا الضالين فقولوا ءامين)).

4. Na biyu: ba dukkan Shi’ah Ithna Ishriyyah ba ne s**a hana yin “A’ameen” bayan kare karatun Fatiha a cikin salla, a’a, akwai wadanda suke yin “A’ameen” bayan Fatiha saboda ingantacciyar ruwayah daga littattafan hadithi na Shi’ah, ga ma ruwayar: Tuusiy ya ruwaito cikin Tahzeebul Ahkam 2: 75/277, ya kuma ruwaito cikin Alis Tibsar 1: 318/1,187, haka nan Muhammadul A’amily ya ruwaito cikin Wsaa’ilush Shi’ah 6/68, dukkansu biyun sun ruwaito kamar haka: ((عن جميل قال: سألت أبا عبد الله عليه السلام عن قول الناس في الصلاة جماعة حين يقرأ فاتحة الكتاب: ءامين. فقال: ما أحسنها! واخفض الصوت بها)).
Babban malamin Shi’ah Abul Qasim Al-Qummiy ya ce cikin littafinsa: Ganaa’imul Ayyam 2/507: ((ونقل عن ابن الجنيد الجواز عقيب الحمد وغيرها، وقواه بعض المتوخرين لصحيحة جميل، قال: سالت ابا عبد الله عن قول الناس جماعة حين يقرا فاتحة الكتاب " ءامين قال ما احسنها واخفض الصوت)).
Haka nan babban malamin Shi’ah Al-Muhaqqiqul Bahraaniy ya ce a cikin littafinsa Al-Hadaa’iqun Naadhirah 8/196 kamar haka: ((ونقل عن ابن الجنيد انه يجوز التأمين عقيب الحمد وغيرها)).

5. Allah muke rokon Ya tsare mu daga sharrin jahilci. Ameen.
Daga Dr Ibrahim jalo jalingo

Kun yarda TAKALMIN SHI yafi kowa AMMA SALATIN SA ne baku yarda yafi na kowa ba. Inna haza lashaiun ajib. (S A W)
15/09/2023

Kun yarda TAKALMIN SHI yafi kowa AMMA SALATIN SA ne baku yarda yafi na kowa ba. Inna haza lashaiun ajib. (S A W)

12/09/2023

Wanda yakawo SALATIN IBRAHIMIYYA baya KARYA,baya kuskure, AMITACCEN ALLAH, bin ABDULLAHI (SAW).

12/09/2023

Ku daina hada SALATIN IBRAHIMIYYA da SALATIL FATI.

Ina nan zuwa Kano da ikon Allah.  GAWUNA is coming, inshallah.
11/09/2023

Ina nan zuwa Kano da ikon Allah.
GAWUNA is coming, inshallah.

26/08/2023

Bazan manta da Sheikh JAFAR MAHMUD ADAM ba kwararre wajen fassara ALQURA'NI da harshen HAUSA.

12/07/2023

GAWUNA is coming.
INSHALLAH.

Address

Central Mosque Sabo Ibadan
Ibadan

Telephone

+2348066784380

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ibrahim Abubakar B Yara posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Ibrahim Abubakar B Yara:

Share

Category