09/03/2026
Assalamu Alaikum
Barkanmu da wannan lokacin Allah ya karba mana ebadunmu
1.Kamar yadda kowa yasani munyi Taron rabon kayan inda aka rabawa marayun wannan foundation kayan sallah da kudin su yakai naira (1,372,600)
Wanda daga baya muka Kara samun Yan complain suma anje an sake Sayo kayan naira (213,000)
Wanda total din abunda kayan su ya k**a (1,585,600)
2.wannan foundation ya samu tallafin buhu 15 na shinkafa mun rabasu ga gidaje 15.
3.wannan foundation ya samarwa Yara marayu katin karbar magani a asibiti kyauta Wanda yanxu haka katin ya zama ready Wanda yanxuma za su iya fara aiki dashi domin an Riga da ansa kudin su
Muna yiwa duk wadanda s**a Bada gudunmawarsu ta kowace hanya Allah ya saka musu da Alheri