10/07/2023
Alhamdulillah.
Kaman yanda mukayi alkawari a 23rd March, 2023 bayan kammala aikin mu na bibiyan zabe a Zamfara, wanda project ne na me zaman kanshi na gidauniyar ku ta ZamTracka, Allah ya nufi mun kammala wannan report me peji 40.
Wannan shine irin shi na farko da wata qungiya mai zaman kanta tayi kacokan akan jiha guda a fadin Nigeria. A cikin report din, mu bayyana irin tsarin da mukayi don wanzar da shirin a fadin jihar, da kuma yin bayani cikakke bisa alqalumma masu muhimanci. Munyi bayani akan yanda kuddi, kimiyya, jami’an tsaro, jami’an INEC da ma duk sauran masu ruwa da tsaki s**ai tasiri akan sakamakon zaben!
Mun kuma qara gaba munyi bayanin yanayin jihar bayan fadin sakamakon zaben da kuma yanda aka yi ta’adi da ta’addanci ga dukiyar al’umma da sunan murna da ganima.
Godia marar adadin ga team din mu da s**ayi aikin zagaye jihar nan wajen samo bayanai kai-tsaye akan sha’anin zaben. ❤️
Zamu wallafa shi a website din mu bayan zama na musamman da INEC da kuma sauran stakeholder akan inganta zabe mai zuwa.
Alhamdulillah!❤️