Jiya DA Yau

Jiya DA Yau Jiya da Yau shafi ne da ke kawo hotuna, labarai da abubuwan tarihi na baya tare da yadda suke a yau. Ku biyo mu domin ganin bambancin Jiya da Yau.

Manufarmu ita ce tuna baya, fahimtar canji, da ganin yadda lokaci ke sauya rayuwa.

"on my part, the battle against apartheid has just begun"One thing about their generation is that they understood the co...
22/05/2026

"on my part, the battle against apartheid has just begun"

One thing about their generation is that they understood the concept of Orcham razor.
In one paragraph, the entire message was communicated.
In today's world, a whole A4 will not be enough to convey the message.

JIYA BA YAU BA...“SHAGO DA ƊAN DUNAWA” WASU SHAHARARRUN ‘YAN DAMBEN ƘASAR HAUSA A SHEKARUN 190sA tarihin gargajiyar Haus...
21/05/2026

JIYA BA YAU BA...

“SHAGO DA ƊAN DUNAWA” WASU SHAHARARRUN ‘YAN DAMBEN ƘASAR HAUSA A SHEKARUN 190s

A tarihin gargajiyar Hausawa, wasan dambe na ɗaya daga cikin manyan wasannin da s**a yi fice tun shekaru aru-aru. Daga cikin fitattun jaruman damben wancan lokaci kuwa akwai shahararrun ‘yan dambe biyu — Shago da Ɗan Dunawa, waɗanda sunayensu s**a yi ƙararrawa musamman a yankin Gusau, Kano da sauran sassan Arewacin Najeriya.

An san su da ƙarfin jiki, jarumtaka da kuma salon dambe mai kayatarwa wanda ke jawo dubban mutane zuwa filin wasa. Karawarsu ta yi matuƙar shahara har ta kai ga mutane suna ta muhawara kan wanene yafi ƙarfi a tsakaninsu.

A shekarar 1957, kamar yadda jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta ruwaito, ance wai an gudanar da wata babbar karawa a tsakanin Shago da Ɗandunawa a birnin Kano. A lokacin, mutane da dama sun yi hasashen cewa Shago ne zai yi nasara saboda ƙwarewarsa da irin sunan da yake da shi a damben gargajiya. Sai dai abin mamaki, al’amura s**a sauya yayin fafatawar, inda Ɗan Dunawa ya nuna bajinta sosai har Shago ya sha wahala ƙwarai a damben, Amma babu tabbacin wannan labari a zahiri hasalima wasu sunce basu taba karawa a dambe ba tsakin su.

Rahotannin sun nuna cewa yawan karawar da s**a yi da juna da kuma tsananin gogayyarsu ya kai ga sun ɗauki alkawarin cewa ba za su sake dambe da juna ba, saboda irin wahala da gajiya da kowannensu ke sha a duk lokacin da s**a haɗu.

A cikin wannan tsohon hoto mai ɗauke da tarihin gargajiya:

Ana ganin Ɗan Dunawa a hannun hagu shine da naɗi a ƙafa

Shago ne a hannun dama,,
👇
Dan Audu mai hagun Mai dama in hagun taƙiya ka koma dama,,,,

Kashe mutum a gafarta ma,,,

Yan maza kunji kidin kututture na bakura duna mahaukaci na yamma da,,,

Mai bugu K**a da azazza,,,

Duna ka ga raina ya ɓaci banga ka buge wani ba, barin amana tsoro yanzu inai maka kuka ba kukan tuwo ba bana fura ba kuka baleri ya datse bayi suna kirarin banza,,,,

Yaro gafarar ka ga Sababi nan dan ba ka san halin kanin Ajali,,,

Gurumzumi abin zub

Address

Gusau

Telephone

+2347012909696

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jiya DA Yau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Jiya DA Yau:

Shortcuts

Share