12/12/2023
*Sanin Hakkin Dake kan khaleefan Tijjaniyya shi ya kamata mufara sani kafin mufara kofafi (3)!!!*
Koh Ina mafita ?
1.Ajiye Banbancin Halara: dole ne dukkan Tijjanawa su karbi dukkan Cigaba, a hannun kowaye yazo, ko da kuwa ba shehin ku Daya ba, Kuma Koda Mahaifinsa muridi ne a Zawiyyar ku, Lura da Girman abun da yazo dashi yafi a kalli Girmansa.
2. Dole ne kowacce a Zawiyya tasan adadin malamanta da Kuma Muridanta, sannan dole ne tasan duka adadin Rassu da take dasu a fadin Duniya tare da daliban Dake karatu a cikinsu Hakan zai taimaka Mana wajan Gane yawanmu tare da samun sauki wajan Tallafawa marasa Karfi dake cikin kowacce Zawiyya, dole ne Sai ansan da mutum sannan za'asan Yana cikin Bukata Koh baida ita.
3. Dole ne a fitar da kungiyar Dalibai Yan Tijjaniyya a Nigeria Mai magana Daya wacce zata kasance karkashin kulawar majalisar shura, hakan zai kawar da cin zarafin dakewa Dalibai a manyan Makarantun Nigeria, Kuma hakan zai sa asamu Tsari Mai kyau wajan Rabawa Tijjanawa tallafin karatu na kasashen waje, hakan Kuma zai iya sawa a duk shekara a bawa wannan kungiya Gurbin tura wasu Dalibai a makarantun Nigeria.
4. Dole ne a kafa kungiyar Lauyoyi, jami'an Tsaro, Likitoci, malaman manyan Makarantu, Yan jarida dukkansu mabiya Darikar Tijjaniyya, domin kuwa wannan zaisa idan angina Asibiti mallakin Tijjaniyya kamar yanda muke fata, to sune zasuyi Aiki a ciki, idan aka Gina jami'a Koh Gidan Jarida s**a Yan Tijjaniyya ne zasuyi Aiki, Lauyoyi kuwa kowa yasan amfanin su ga irin cin Kashin Dakewa Yan Tijjanawa a Nigeria.
Wadannan sune kadan daga cikin shawarwarin da Nike bawa Yan uwana Tijjanawa muyi, matukar mukayi wannan Tsari ba'a taimakemu ba, Sai mu fito muyi korafi domin kuwa anyi Tsari Kuma ammallaki dukkan takardun da ya kamata Amma khaleefa Yaki taimakawa!!!
Allah yasa mudace, Allah yabamu ikon Halacci ka rabamu da Butulci
✍️
Abdullahi Adam
Jama'a