Nahuche Class Of 2017

Nahuche Class Of 2017 Mun bude wannan page domin isar da saqon wannan kungiya cikin sauqi tare da saka wasu labarai ingan tattu

SAƘON TA’AZIYYANACO 2017 TA MIƘA SAƘON TA’AZIYYA GA ƊAYA DAGA CIKIN MEMBOBINTAƘungiyar Tsofaffin Ɗalibai ta Shekarar 201...
05/09/2026

SAƘON TA’AZIYYA

NACO 2017 TA MIƘA SAƘON TA’AZIYYA GA ƊAYA DAGA CIKIN MEMBOBINTA

Ƙungiyar Tsofaffin Ɗalibai ta Shekarar 2017 (NACO 2017 – Nahuche Class of 2017), ƙarƙashin jagorancin Nurse Kamaluddeen Aminu, na miƙa saƙon ta’aziyyarta bisa rasuwar Malam Lawali Yargungun, mahaifin ɗaya daga cikin membobin ƙungiyar, Sanusi lawali.

Ƙungiyar ta bayyana matuƙar alhininta da jimamin wannan babban rashi, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayin, ‘yan uwa, abokan arziki da daukacin al’ummar da wannan rashi ya shafa.

A yayin miƙa ta’aziyyar, Shugaban Ƙungiyar ya bayyana rasuwar Malam Lawali Yargungun a matsayin babban rashi ga iyalinsa da kuma al’umma baki ɗaya, duba da irin gudunmawar da marigayin ya bayar wajen koyarwa, tarbiyya da hidima ga al’umma.

Ya ƙara da cewa, rasuwar mutum mai irin wannan matsayi ba ta tsaya ga iyalinsa da ‘yan uwansa kaɗai ba; illa tana shafar dukkan waɗanda s**a taɓa amfana da iliminsa, tarbiyyarsa da kyakkyawar mu’amalarsa.

A madadin Shugabanni da daukacin membobin NACO 2017, muna miƙa ta’aziyya ta musamman ga ɗan uwanmu Sanusi Lawali da sauran iyalan marigayin. Muna roƙon Allah Ya ba su haƙuri da juriya wajen jure wannan babban rashi.
Allah ya gafarta masa
Allah ya karbi kyakkyawan ayyukan sa.
Ameen ya Allah

23/03/1448AH
05/09/2026

✍️: Najeeb Sani
Publicity Secretary NACO 2017

Ƙungiyar Tsofaffin Ɗalibai ta Shekarar 2017 (NACO 2017 – Nahuche Class of 2017) na miƙa sakon taya murna ga ɗaya daga ci...
22/08/2026

Ƙungiyar Tsofaffin Ɗalibai ta Shekarar 2017 (NACO 2017 – Nahuche Class of 2017) na miƙa sakon taya murna ga ɗaya daga cikin membobinta, Mataimakin Sakataren Ƙungiyar, KABIRU SULAIMAN (CHIROMAN NAHUCHE), bisa nasarar kammala karatunsa na High National Diploma (HND) a Business Administration And Management

Wanda ya kammala wannan karatu ne a ranar Juma'a, 08/03/1448AH - 21/08/2026, a Federal Polytechnic Kaura Namoda

Wannan nasarar kammala karatun wata babbar shaida ce ta jajircewa, ƙwazo da himma wajen neman ilimi da cigaban kai, Haƙiƙa Ƙungiyar NACO 2017 na alfahari da wannan gagarumar nasara, tare da fatan za ta zama wata hanya ta cigaba da yi wa al'umma hidima.

Amadadin Shugabanni da daukacin Mambobin NACO 2017, muna taya CHIROMAN NAHUCHE murna tare da yi masa fatan samun nasarori mafi girma a rayuwarsa ta ilimi da sana'a.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanya albarka a cikin ilimin da ya samu, ya ba shi ikon amfani da shi wajen yiwa addinin Musulunci da al'umma hidima, Ya kuma ƙara masa buɗi na alheri da dacewa a dukkan al'amuransa.

Allah ya sanya albarka a cikin abin da aka karanta. Allah yasa ya amfana da iliminsa, ya kuma amfanar da al'ummar Musulmi baki ɗaya.
Allahumma Amiin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

Congratulations once again, CHIROMAN NAHUCHE

👈: Najeeb Sani
Publicity Secretary
NACO 2017
09/03/1448AH - 22/08/2026M

Ƙungiyar Tsofaffin Ɗalibai ta Shekarar 2017 (NACO 2017 – Nahuche Class of 2017) na miƙa sakon taya murna ga ɗaya daga ci...
06/08/2026

Ƙungiyar Tsofaffin Ɗalibai ta Shekarar 2017 (NACO 2017 – Nahuche Class of 2017) na miƙa sakon taya murna ga ɗaya daga cikin shugabanninta, Mataimakin Sakataren Ƙungiyar, Abubakar Bature (A Square), bisa nasarar kammala karatunsa na Diploma a fannin Community Health.

Wanda ya kammala wannan karatu ne a ranar Talata, 21/02/1448AH - 04/08/2026, a Gusau College of Health Science and Technology, Gusau, Jihar Zamfara.

Wannan nasarar kammala karatun wata babbar shaida ce ta jajircewa, ƙwazo da himma wajen neman ilimi da cigaban kai, Haƙiƙa Ƙungiyar NACO 2017 na alfahari da wannan gagarumar nasara, tare da fatan za ta zama wata hanya ta cigaba da yi wa al'umma hidima.

Amadadin Shugabanni da daukacin Mambobin NACO 2017, muna taya Abubakar Bature (A. Square) murna tare da yi masa fatan samun nasarori mafi girma a rayuwarsa ta ilimi da sana'a.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanya albarka a cikin ilimin da ya samu, ya ba shi ikon amfani da shi wajen yiwa addinin Musulunci da al'umma hidima, Ya kuma ƙara masa buɗi na alheri da dacewa a dukkan al'amuransa.

Allah ya sanya albarka a cikin abin da aka karanta. Allah yasa ya amfana da iliminsa, ya kuma amfanar da al'ummar Musulmi baki ɗaya.
Allahumma Amiin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

Congratulations once again, A Bature

👈: Najeeb Sani
Publicity Secretary
NACO 2017
23/02/1448AH - 06/08/2026M

02/06/2026

5th Annual Sallah Get-Together Organized By The Nahuche Class of 2017 Under the Leadership of Nurse Kamaluddeen Aminu

Closing Prayer
Mukhtar Rabiu Nahuche

Karin wasu hotona na 5th Annual Sallah get together wanda ƙungiyar tsofaffin ɗalibai na shekarar 2017 s**a gabatar ƙarƙa...
02/06/2026

Karin wasu hotona na 5th Annual Sallah get together wanda ƙungiyar tsofaffin ɗalibai na shekarar 2017 s**a gabatar ƙarƙashin jagoranci Nurse Kamaluddeen Aminu

Karin wasu hotona na 5th Annual Sallah get together wanda ƙungiyar tsofaffin ɗalibai na shekarar 2017 s**a gabatar ƙarƙa...
02/06/2026

Karin wasu hotona na 5th Annual Sallah get together wanda ƙungiyar tsofaffin ɗalibai na shekarar 2017 s**a gabatar ƙarƙashin jagoranci Nurse Kamaluddeen Aminu

Amadadin kwamitin gabatar da taron sada zumunci na kungiyar Tsofaffin Daliban Nahuche ta shekarar 2017 (NACO 2017), muna...
02/06/2026

Amadadin kwamitin gabatar da taron sada zumunci na kungiyar Tsofaffin Daliban Nahuche ta shekarar 2017 (NACO 2017), muna miƙa saƙon godiya na musamman ga dukkan mahalarta wannan Sallah Get-Together na 2026 karo na biyar (5th Annual Sallah Get Together)

‎Muna godiya ga shugabanni da dukkan mambobinmu da s**a samu damar halarta tare da bayar da gudummawar su wajen tabbatar da nasarar wannan taro.

Haka kuma muna matuƙar godiya ga waɗanda s**a gabatar da maƙala, da waɗanda s**a yi sharhi, haɗi da waɗanda s**a bada shawarwari da gudummawar tunani masu amfani don ci gaban ƙungiyarmu.

‎Kasancewar mu tare a yau ya nuna muhimmancin haɗin kai, zumunci da ƙaunar juna da ke tsakanin mambobin wannan aji. Muna fatan abubuwan da aka tattauna za su zama tubalin gina kyakkyawar makoma ga kowa da kowa.

‎Allah Maɗaukakin Sarki ya saka wa kowa da alkhairi, ya albarkaci zumuncinmu, ya ƙara mana haɗin kai da fahimtar juna, ya kuma ba mu ikon ganin mun cimma manufofin da muka sanya a gaba.

‎Mun gode da halartarku, bada lokacinku, da goyon bayan da kuke bai wa NACO 2017.

Insha Allah ‎Tare zamu samu cigaba, tare zamu samu nasara.

Najeeb Sani
Publicity Secretary NACO 2017
15/12/1447AH
01/06/2026M

Address

By Pass Gusau
Gusau
447958

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nahuche Class Of 2017 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Nahuche Class Of 2017:

Shortcuts

Share