04/06/2026
CNG Ta Nuna Damuwa Kan Yadda Gwamnati Ke Nuna Bambancin Kulawa Tsakanin Wadanda Aka Sace A Oyo Da Borno
Gamayyar Ƙungiyoyin Arewacin Najeriya (CNG) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro da su tabbatar da cewa duk waɗanda matsalar tsaro ta shafa a Najeriya na samun kulawa iri ɗaya ba tare da la’akari da yankin da s**a fito ba.
Shugaban ƙungiyar, Kwamared Jamilu Aliyu Charanchi, ya bayyana haka yayin wata hira da Daily Trust ranar 3 ga Yunin 2026, inda ya nuna damuwa kan abin da ya bayyana a matsayin bambancin yadda ake mayar da hankali kan sace ɗalibai a jihohin Oyo da Borno.
A cewarsa, rahotanni sun nuna cewa a ranar 15 ga Mayu, 2026, an sace ɗalibai da malamai kusan 46 daga wasu makarantu da ke ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo. Hakazalika kuma, an yi garkuwa da ɗalibai 42 daga makarantar M***a Primary da Junior Secondary School da ke Askira Uba a jihar Borno a wannan rana.
Charanchi ya ce CNG na Allah wadai da duk wani nau’in ta’addanci, garkuwa da mutane da kashe-kashe a ko’ina cikin Najeriya, yana mai cewa rayuwar kowane ɗan ƙasa tana da muhimmanci kuma ta cancanci kariya daga gwamnati.
Ya bayyana cewa ƙungiyar ba ta ce a rage kulawar da ake bai wa jihar Oyo ba ne, sai dai tana kira da a nuna tausayi, goyon baya da kulawa iri ɗaya ga waɗanda abin ya shafa a Borno da sauran sassan ƙasar nan.
“Duk inda aka sami matsalar tsaro a Najeriya, gwamnati dole ta nuna damuwa iri ɗaya saboda babu rayuwar da ta fi wata muhimmanci,” in ji Charanchi.
Shugaban na CNG ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta ƙara ƙaimi wajen ceto waɗanda aka sace, tare da samar da ingantacciyar dabarar tsaro domin magance matsalar ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran laifukan tashin hankali da ke addabar ƙasar.
Haka kuma ya nemi a ƙarfafa tsaron makarantu da yankunan karkara, tare da inganta tattara bayanan sirri domin dakile ayyukan masu aikata laifuka a faɗin Najeriya.
A ƙarshe, Charanchi ya ce idan gwamnati ta ci gaba da bai wa dukkan yankunan ƙasar kulawa iri ɗaya wajen matsalolin tsaro, hakan zai taimaka wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa da dawo da amincewar jama’a ga hukumomi.