Gapsobag

Gapsobag Gandu Primary School Old Boys Association.

10/05/2020

BADA GIDAN HAYA GA MASU BAUTAR COCI?
Tambaya
Assalamu Alaikum. Malam dan Allah miye matsayin Musulmi da ya gina hotel kuma yana baiwa kafirai haya suyi choci?
Amsa
Wa'alaikum assalam, Bai halatta ba, saboda Allah madaukakin sarki ya hana taimakawa mai aikin sabo. Aya ta biyu a cikin suratul Ma'ida tana cewa: "Kuma ku dinga tamakekeniya wajan aikata alkairi, Amma kada ku yi tamakekeniya wajan aikata sabo". Ibadar COCI shirka ce kamar yadda ayoyi da yawa a suratul Ma'ida s**a siffanta Wanda yake bautawa annabi Isa da kafiri.
Allah Ne mafi Sani.
Amsawa:- Dr. Jamilu Zarewa

SUNAYE: Jihohi da kananan hukumomin da za su iya fadawa matsalar amai da zawo a kasar nan - Premium Times
06/07/2019

SUNAYE: Jihohi da kananan hukumomin da za su iya fadawa matsalar amai da zawo a kasar nan - Premium Times

Premium Times News delivered in indegineous language, Hausa.

25/05/2019

ME IYAYE SUKAFI BUQATA A WAJEN DANSU BAYAN SUN MUTU?
Tambaya
Assalamu Alaikum!!!
Allah yasakawa malam da mafificin alkhairi
malam tambayata itace idan iyayen mutum s**a rasu mai s**afi bukata daga gareshi? Nagode
Amsa:
To Dan Uwa, akwai hadisan da s**a yi umarni da yi musu sallah da nema musu gafara bayan sun mutu, da yi musu sadaka, wannan shi ne maganar mafi yawan malamai, har wasu marubuta ma sun hakaito ijma'i akan haka. saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi" Dan mutum yana daga cikin aikinsa" Abudawud ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi a sahihu sunani-abi-dawud hadisi mai lamba ta : 2528.
A wani hadisin Kuma, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : "Idan dan'adam ya rasu ayyukansa s**an yanke sai dayan abubuwa guda uku : sadaka mai gudana, ko ilimin da ake amfana da shi, ko da nagari da yake masa addu'a" kamar yadda Tirmizi ya rawaito shi kuma ya inganta shi a hadisi mai lamba ta :1376. A karkashin wadannan hadisai, zamu iya fahimtar cewa, mafi girman abinda iyaye suke buqata a wajen dansu bayan sun mutu shine addu'a.
Don neman Karin bayani : duba majmu'ul fataawa :24\366 da Nailul Audaar 4\112 da Ahakamul jana'iz shafi na : 171. Allah shine mafi sani
Abu-Basheer 12/5/2019

11/03/2019

ZAMAN GULMAR SHUWAGABANNI DA 'YAN SIYASA
Tambaya
Assalãmu Alaykum, Yaa Shaykh, menene hukuncin magana akan shugabanni da 'yan siyasa? Shi ma gulma ne ko akwai banbanci idan mutumin yana da nauyin yiwa al'umma shugabanci da hidima? Jazakumullahu Khayran
Amsa
Wa'alaykumussalam, To dan'uwa Allah da manzonsa sun haramta cin naman mutane, sannan malamai suna cewa: gulmar shuwagabanni da malamai ta fi tsananin haramci, saboda cin naman shuwagabanni zai jawo ayi musu tarzoma, kamar yadda cin naman malami zai jawo a raina ilimi, saidai akwai wuraren da ya halatta a ci naman mutane saboda maslaha, kamar idan aka zalunci mutum to ya halatta idan zai kai kara ya bayyana zaluncin da aka yi masa, haka nan idan ya ga wani sharri yana so a taimaka masa wajan gusar da shi to ya halatta ya fadi sunan mai laifin, kamar yadda kuma ya hallata ayi gulmar mutumin da ya shahara da aikata sabo da fasikanci, don a guji sharrinsa. Duba Azkar: 489 da kuma Majmu'ul fataawa 28\221.
A bisa abin da ya gabata za mu fahimci cewa: duk kasar da ake kafa shugaba ta hanyar zabe, to ya hallata mutane su tattauna matsalolin shugaban da yake kai, domin tunanin kawo canji a zabe mai zuwa, musamman idan shugaban ya kasance azzalumi kuma fasiki mai yawan aikata sabo, saidai ya wajaba maganar ta su ta zama gwargwadon bukata.
Allah ne mafi sani.
27/3/2015
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

08/03/2019

WA YAKAMATA NA ZABA A MATSAYIN SHUGABA???
Tambaya:
Assalamu Alaikum
Dafatan Kana Lafiya, Duba Da Yadda Zaben Nigeria Na 2019 Ya Gabato Gadan Gadan, Tambayane Shine Wani Siffofi Ya Kamata Mutum Yayi La'akari Dashi Wajen Zaben Shugaba. Na Gode
Amsa:
Wa Alaikum Assalam
To Dan Uwa, Ina Maka Wasiyya Dajin Tsoron Allah Wajen Zaben Shugaba Nagari. Wajibine Kayi
La'akari Da Wadannan Siffofi Wajen Zaben Shugaba. Dolene Yazamanto:
1. Mutum Mai Addini
2. Mai Kwatanta Adalci
3. Mai Rikon Amana
4. Mai Cika Alqawari
5. Mai Gaskiya
6. Mai Tausayi
7. Mai Ilimi
8. Mai Kyakkyawan Mu'amala
Idan Aka Samu Mutum Mai Kwatanta Wadannan Abubuwa Guda Takwas To Babu Laifi Idan Aka Za6eshi A Matsayin Shugaba.
A Karkashin Wannan, Ya Zamo Wajibi A Gareka Ka Nisanci Za6an Shugabanda:
1. Baida Addini
2. Maqaryaci (Mara Gaskiya)
3. Maciyin Amana
4. Mayaudari
5. Marar Adalci
6. Marar Tausayi
7. Marar Ilmi
8. Wanda Baida Kyakkyawan Mu'amala
Duk Wanda Ka Za6a Saboda Son Zuciya Matuqar
Yaci Za6e Kuma Yaci Amanar Qasa Da Zaluntar Talakawansa, Allah Zai Tambayeka Akan Hakan A Ranar Alqiyama.
Allah Ya Za6a Mana Shugabanni Nagari.
Ibrahim Kuna Ibrahim 22/2/2019

01/03/2019

WALIMAR CIN ZABEN BUHARI ?
Tambaya
Assalamu alaikum. Malam Ina yi maka fatan alkairi. Ina da tambaya! shin menene hukuncin wadanda s**a tara kudi s**a yi walima don murnar Buhari yaci zabe? domin wasu suna ganin cewa bidi'ah ne hakan kamar ta Mauludi.
Amsa
Wa'alaikumus Salam
To da'uwa Allah ya shar'anta godewa masa a bisa ni'imomin da ya yi, kamar yadda aya ta (114) a suratun Nahli take nuni zuwa hakan.
Cin zaben Buhari ni'ima ce a mahangar da yawa daga cikin 'yan Nigeria saboda zaton da suke kyautata masa da kuma matsalolin da s**a dandana a gwamnatin da ya kayar.
Annabi (s.a.w) ya kasance idan ya dawo daga tafiya , yana yanka rakumi, ya kira mutane su zo su ci, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2923.
Ana iya godewa Allah da nau'uka daban-daban na ibada, kamar azumi da yanka, da ciyar da miskinai.
Wannan yasa babu laifi idan mutum Allah ya yi masa ni'ima ya gode masa, don ya kara masa, kuma ya taimake shi wajan yin amfani da ita ta fuskar da ta dace.
Don neman Karin bayani duba : Al-mausu'a Alfiqhiyya 26/180, da fatawaa Ibnu-bazz 5\388.
A bisa abin da ya gabata walimar cin zaben Buhari ta halatta mutukar ba'a kudurce cewa ibada ce mai zaman kanta ba, ko kuma an aikata bidi'o'i a lokacin yinta.
Yin walima saboda samun wata nasara, ya bambanta da maulidi, saboda shi maulidi ana yinsa a matsayin ibada ta musamman, tare da kebance kwanaki na musamman, wannan ya sa ya zama bidi'a, saboda babu hujjar da ta karfafe shi.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
8\4\2015

11/01/2019

ZAN IYA JAN CARBI, KO KO BIDI'A NE?
Tambaya:
Assalamu Alaikum. Tambaya. Allah ya gafartawa Mal. Na kasance ina amfani da charbi (Tasbaha) domin yana tunatar dani wajen ambaton Allah a kowane lokaci.
Ina matsayin haka a sharia ?
Amsa:
To dan'uwa jan carbi ba bidi'a ba ne, saboda duk da cewa babu shi a zamanin Annabi ﷺ hakan ba zai sa ya zama bidi'a ba, saboda wanda yake amfani da shi ba ya nufin cewa ibada ce mai zaman kanta, yana amfani da shi ne, don ya kiyaye adadin zikirinsa.
Yin amfani da 'yan yatsu shi ne yafi, saboda hadisi ya yi nuni cewa : za'a ba su dama su yi magana, ranar alkiyama, kamar yadda Tirmizi ya rawaito kuma Albani ya inganta shi a hadisi mai lamba ta: 3486, don haka za su yi maka shaidar abin da ka yi na alkairi, sabanin carbi.
Sannan sau da yawa za ka ga mutum yana jan carbi amma hankalisa yana wani wajen, sabanin idan da hannu yake yi.
Jan carbi yakan iya sanya wasu su yi riya, saboda wasu suna ratayawa ne a wuya don a gane su zakirai ne. Annabi ﷺ yana yin tasbihi da hannunsa na dama kamar yadda ya tabbata a hadisin Abu- dawud mai lamba ta: 1286, wanda Albani ya inganta, sai dai wasu malaman suna cewa in ya yi da hagu ma yayi, tare da cewa yi da dama shi ne ya fi.
Sai dai duk da dalilan da s**a gabata, mutum zai iya jan carbinsa, tun da jan carbi ba ibada ce mai zaman kanta ba, b***e ace ya zama bidi'a, ga shi kuma ba'a samu wani hadisi da ya hana ba, tare da cewa yi da hannu shi ne yafi.
Don neman Karin bayani duba: Majmu'ul fataawa 22\187. Da Lika'ul maftuh na Ibnu-uthaimin 3\30.
Allah ne mafi sani
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

28/12/2018

*_WANDA YA GANNI A MAFARKI ZAI GANNI A FILI!!!_*
*Tambaya:*
Akramakallah shin akwai hadisin da ya tabbata daga manzon Allah (S.A.W) cewa yace '' man ra'ani fil manami fasayarani fil yaqzwa''wato wanda ya ganni a mafarki to tabbas zai ganni a fili. To shin malam hakan tana yiwuwa, kuma har ma Annabin ya bada wata falala? Almajirinka daga Beli.
*Amsa*
Dan'uwa wannan hadisi ne tabbatacce daga Annabi ﷺ kamar yadda Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta: 6592.
Saidai malamai sun yi sabani game da lafazin zai ganni a fili, wasu sun ce: ma'anarsa: zai gan shi rana alkiyama da sifa ta musamman, wasu kuma sun ce zai gan shi a duniya, saidai wannan zancen yana da rauni sosai, tun da hadisi ya tabbata cewa annbawa suna cikin kabarinsu, wasu malaman kuma sun ce hadisin yana Magana ne akan wadanda s**a zo a zamaninnsa, ma'ana duk wanda ya gan shi a mafarki, to zai hadu da shi.
Malamai suna cewa abin da ake nufi shi ne ka gan shi da siffofinsa wadanda s**a tabbata a hadisi, inda za ka gan shi bakikkirin ba gemu, ko da mafarkin ya nuna maka annabi ne to ba shi ba ne, tun da hakan ya sabawa siffarsa a hadisi, wannan ya sa idan mutum ya zo ya cewa: Muhammad dan Siirin R.A, ya ga Annabi ﷺ a mafarki yakan ce masa siffanta min shi, in ya fadi kamannin da s**a sabawa hadisai, sai ya ce ba shi ka gani ba, an rawaito kwatankwacin haka daha Ibnu Abbas.
Ba'a karbar wani hukunci ko wata falala daga Annabi ﷺ a cikin mafarki, saboda hakan yana nuna tawayar addini, tare da cewa aya ta uku a cikin suratul Ma'ida ta nuna cikar addini, tun fiye da shekara dubu.
Don neman Karin bayani duba : Alminhaj na Nawawy 1/50 da kuma Fathul-bary 12/386.
Allah ne mafi sani.
30\12\2014
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

20/12/2018

_HUKUNCIN YIN SALLAR JAM'I A GIDA !!!_*
*_Tambaya_*
Assalamu alaikum. Malam mene hukuncin sallar namiji da ba ya son zuwa masallaci jam'i saidai ya tara iyalinsa a gida ayi sallah tare?
*_Amsa_*
Wa alaikum assalam
To 'yar'uwa Malamai sun yi sabani game da sallar jam'i a masallaci.
1. A wajan malaman Malikiyya zuwa sallar jam'i sunna ne saboda fadin Annabi S. A.W. "Sallar jama'a tafi sallar mutum daya da lada ashirin da bakwai" hadisin yana nuna ingancin sallar wanda ya yi sallah shi kadai, tun da an tabbatar masa da lada daya.
2. Ya wajaba yin sallah a masallatai a cikin jama'a saboda fadin Annabi (SAW) "Na yi niyyar na yi umarni a tsayar da sallar jam'i, ni kuma na je na kona gidajan wadanda ba Sa halarta sallah a masallaci" wannan ita ce maganar Malamai da yawa.
Ibnu-Mas'ud yana cewa: "Babu wanda yake kin zuwa sallar jam'i sai munafiki, wanda aka san shi da munafunci, akan kawo mutum ranga-ranga ba shi da lafiya a tsayar da shi a tsakanin Sahu".
Wani Makaho ya zo wajan Annabi (SAW) ya nemi ya yi masa izni ya yi sallah a gida saboda ba shi da Jagora, ya ba shi izni, bayan ya tafi sai ya Kira shi ya ce masa kana jin kiran sallah? sai ya ce E, sai ya ce to ka amsa".
Allah yana cewa a Suratul Bakara aya ta (43): "Kuma ku yi sallah tare da masu yin sallah"
A bisa dalilan da s**a gabata za mu fahimci cewa: Yin sallar jam'i a masallaci shi ne abin da Shari'a ta zo da shi, kuma wajibi ne ga wanda yake da iko, tun da ga shi har Annabi (SAW) ya yi niyyar zai kona gidan wadanda ba sa halarta.
Idan akwai nisa tsakaninsa da masallaci ko kuma yana da lalura ba za'a ce ya aikata haramun ba in ya yi sallah a gida tare da iyalansa saboda fatawar Malikiyya da ta gabata da kuma aya ta karshe a suratul Hajj wacce take nuna sauki da rashin kunci a addinin musulunci.
Allah ne mafi sani.
*_Dr. Jamilu Zarewa_*
27/06/2018

12/12/2018

SAYAR DA KAYA A WURIN DA AKA SAYA !

Tambaya :

mutum ne zai kawo mota wacce tayi hatsari sai wani ya siya misali dubu 600'000 ,to shi wanda ya siyar yana wajan zai ga an siyar da ita kamar million daya.

Amsa :
Game da tambayarka da ka yi, bai halatta mutum ya sayar da abin da ya saya ba, a wurin da ya yi sayayyar, Annabi s.a.w. ya haramta hakan, kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 3499,
Sharia ta haramta hakan ne, saboda zai iya bude hanyar hassada da kiyayya tsakanin masu cinikayya.
Allah ne mafi sani

Jamilu Zarewa
5\6\2015

01/11/2018

Hi

28/08/2018

_HUKUNCIN YIN SALLAR JAM'I A GIDA !!!_*

*_Tambaya_*

Assalamu alaikum. Malam mene hukuncin sallar namiji da ba ya son zuwa masallaci jam'i saidai ya tara iyalinsa a gida ayi sallah tare?

*_Amsa_*
Wa alaikum assalam

To 'yar'uwa Malamai sun yi sabani game da sallar jam'i a masallaci.

1. A wajan malaman Malikiyya zuwa sallar jam'i sunna ne saboda fadin Annabi S. A.W. "Sallar jama'a tafi sallar mutum daya da lada ashirin da bakwai" hadisin yana nuna ingancin sallar wanda ya yi sallah shi kadai, tun da an tabbatar masa da lada daya.

2. Ya wajaba yin sallah a masallatai a cikin jama'a saboda fadin Annabi (SAW) "Na yi niyyar na yi umarni a tsayar da sallar jam'i, ni kuma na je na kona gidajan wadanda ba Sa halarta sallah a masallaci" wannan ita ce maganar Malamai da yawa.
Ibnu-Mas'ud yana cewa: "Babu wanda yake kin zuwa sallar jam'i sai munafiki, wanda aka san shi da munafunci, akan kawo mutum ranga-ranga ba shi da lafiya a tsayar da shi a tsakanin Sahu".
Wani Makaho ya zo wajan Annabi (SAW) ya nemi ya yi masa izni ya yi sallah a gida saboda ba shi da Jagora, ya ba shi izni, bayan ya tafi sai ya Kira shi ya ce masa kana jin kiran sallah? sai ya ce E, sai ya ce to ka amsa".

Allah yana cewa a Suratul Bakara aya ta (43): "Kuma ku yi sallah tare da masu yin sallah"

A bisa dalilan da s**a gabata za mu fahimci cewa: Yin sallar jam'i a masallaci shi ne abin da Shari'a ta zo da shi, kuma wajibi ne ga wanda yake da iko, tun da ga shi har Annabi (SAW) ya yi niyyar zai kona gidan wadanda ba sa halarta.
Idan akwai nisa tsakaninsa da masallaci ko kuma yana da lalura ba za'a ce ya aikata haramun ba in ya yi sallah a gida tare da iyalansa saboda fatawar Malikiyya da ta gabata da kuma aya ta karshe a suratul Hajj wacce take nuna sauki da rashin kunci a addinin musulunci.

Allah ne mafi sani.

*_Dr. Jamilu Zarewa_*

27/06/2018

Address

Gombe

Telephone

08037432182

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gapsobag posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share