Ailim Foundation Gombe

Ailim Foundation Gombe Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Ailim Foundation Gombe, Non-Governmental Organization (NGO), Gombe.

Ailim Foundation Gombe is a non profit humanitarian organization dedicated to supporting, the needy, sick and vulnerable through charity, compassion, and community service.

01/06/2026

Alhamdulillah!

Muna farin cikin sanar da al’umma cewa an yi nasarar gudanar da aikin tiyatar yarinyar da AILIM Foundation Gombe ta dauki nauyin kula da lafiyarta.

Bayan kiran da aka yi domin neman taimako ga wannan yarinya, wanda ya jawo hankalin al’umma da dama, Founder na AILIM Foundation Gombe, Alhaji Ibraheem Mohammad Liman ya dauki cikakken nauyin kula da lafiyarta tare da biyan kudin tiyatar da sauran bukatun jinyar.

A yau, wakilan AILIM Foundation Gombe sun kai ziyara asibiti domin duba halin da take ciki bayan tiyatar. Mun samu labarin cewa cikin ikon Allah an yi nasarar aikin kuma tana samun sauki a hankali.

Har ila yau, Foundation din na ci gaba da daukar nauyin zaman ta a dakin jinya na musamman har zuwa lokacin da likitoci za su tabbatar da cikakkiyar lafiyarta wanda muke fatan kasancewar shi nan kusa.

Muna gode wa duk wadanda s**a yi addu’a da nuna damuwa game da lamarin, Muna rokon Allah SWT Ya ba ta cikakkiyar lafiya, Ya saka da alheri ga duk masu hannu wajen taimakonta🤲

Ailim Foundation Gombe Aikin Alkhairi Bazai Tsayaba In sha Allah 🔥💪

AlhamdulillahCikin ikon Allah da taimakonshi, shugaban AILIM FOUNDATION GOMBE, Alhaji Ibraheem Mohammad Liman ya fara da...
24/05/2026

Alhamdulillah
Cikin ikon Allah da taimakonshi, shugaban AILIM FOUNDATION GOMBE, Alhaji Ibraheem Mohammad Liman ya fara daukar matakin kula da lafiyar wannan baiwar Allah tare da tura kudin da za a fara gudanar da aikin jinyarta.

Wannan na zuwa ne bayan ganin halin da take ciki da kuma kira da al’umma s**a yi domin a taimaka mata ta samu lafiya.

Muna fatan wannan zai zama sanadin samun sauki da waraka cikin ikon Allah, Ailim Foundation Gombe za ta ci gaba da bibiyar lafiyarta har zuwa lokacin da za a samu cigaba mai kyau in sha Allah.

Hakika taimakon marasa lafiya da masu bukata na daga cikin manyan manufofin gidauniyar mu.

Muna addu’ar Allah SWT Ya baiwa wannan baiwar lafiya cikakkiya, Ya saka da alkhairi ga duk masu taimakon al’umma🤲

AILIM FOUNDATION GOMBE
Aikin Alkhairi… ba zai tsaya ba In sha Allah💪

A yau mun samu kira mai taba zuciya game da wata baiwar Allah da take fama da matsananciyar lalura, lamarin da ya jawo t...
22/05/2026

A yau mun samu kira mai taba zuciya game da wata baiwar Allah da take fama da matsananciyar lalura, lamarin da ya jawo tausayi da damuwa ga al’umma da dama.

Wannan kira dai an yi shi ne domin neman taimako daga fitaccen mai taimakon al’umma wato Engr Aliyu Mohammed Kombat, wanda aka sani da tsayawa wajen taimakon marasa lafiya da masu bukata a lokutan gaggawa.

Cikin ikon Allah, shugaban AILIM FOUNDATION GOMBE, Alhaji Ibraheem Mohammad Liman bayan ganin wannan kira da kuma irin kyawawan ayyukan jin kai da taimakon al’umma da Engr Aliyu Mohammed yake yi ya dauki nauyin kula da wannan baiwar Allah domin ganin ta samu cikakkiyar kulawa da magani in sha Allah.

Wannan na daga cikin manufofin AILIM FOUNDATION GOMBE na:
-Taimakawa marasa lafiya
-Tallafawa masu buƙata
-Rage radadin rayuwa ga al’umma!

Hakika idan mutane masu hali s**a hada kai wajen taimakon jama’a za a samu sauyi mai girma a cikin al’umma.💪

Muna addu’ar Allah SWT Ya baiwa wannan baiwar lafiya cikakkiya Ya saka da alkhairi ga duk masu taimakon jama’a, musamman Engr Aliyu Mohammed Kombat da Alhaji Ibrahim Muhammad Liman🤲

Ku ci gaba da bibiyar Ailim Foundation Gombe domin ganin ayyukan alkhairi da tallafawa al’umma da muke gudanarwa a fadin jihar Gombe.

Address

Gombe

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ailim Foundation Gombe posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share