27/11/2025
Assalamu Alaikum wa Rahmatullah.
A madadin Alhaji Munir Ibrahim Dankwambo (Jagaban Tula) da iyalansa gaba ɗaya, cikin alhini tare da matuƙar kaduwa, muna mika ta’aziyyarmu ga Iyalan Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Darikar Tijjaniyya, da daukacin Al’ummar Musulmi na duniya, bisa rasuwar fitaccen Malaminmu, Jagoranmu, Uban al'umma, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yaɗa addinin Musulunci, tarbiyya da koyar da alheri.
Tarihi ba zai taɓa mantawa da irin gudummawar Marigayin ga al’ummar Musulunci ba. Ya kasance haske, ginshiƙi, kuma madogara ga darikar Tijjaniyya da Musulunci gaba ɗaya.
Rasuwarsa babban rashi ne ga ƙasa, ga al’umma, ga malamai, da kowane talibin ilimi da ya amfana da hikimarsa, darussansa, da jajircewarsa. Hakika mun yi rashin fitila, mun yi rashin shugaba, mun yi rashin jagora.
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya jikansa da mafi girman rahama, Ya yafe masa kurakuransa, Ya haskaka kabarinsa, Ya kara daukaka darajarsa, Ya kuma sanya mu da shi cikin rahamarsa a ranar lahira. Allah Ya ba iyalansa, almajiransa, da dukkan mabiyansa haƙuri, juriya da ladabi wajen ci gaba da riƙe tutar alherinsa.
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.
Signed:
Zakariya Abubakar Hussaini
(Chairman, Munir Dankwambo Foundation)
Madadin ’Yan Uwa da Iyali.