21/01/2026
DAGA FADAR MAI MARTABA SARKIN DUTSE
A yau Laraba MAI MARTABA SARKIN DUTSE ALH. (Dr.) MUHAMMAD HAMIM NUHU SANUSI, CFR ya karɓi baƙuncin;
1. Sabon Kwamishin ‘Yan Sandan Jihar Jigawa CP. Dahiru Muhammed da Jama’arsa, da
2. Kwamandan Rundunar Hisbah na Jihar Jigawa Dr. Muhammad Fa’iz Bashir da Jama’arsa,
3. Ɗaliban Sashen Ilimi da suke koyan Tarihi wato (History) dake Jami’ar Ado Bayero dake Kano bisa jagorancin Shugaban Sashen Dr. Halliru Surajo.
Dalilin wannan Ziyara tasu kuwa shi ne domin gabatar da kawunansu ga Uban Ƙasa kana da neman tabarraki da Addu’ah ta fatan alheri bisa wannan jogoranci nasu.
Mai Martaba Sarki ya fara da yi musu maraba sannan ya musu godiya bisa wannan ziyara da s**a kawo wannan Fada mai tarin Albarka. Ya ƙara da godewa Mai Girma Gwamna bisa kafa wannan runduna ta Hisbah domin ƙara tsaftace Jihar mu mai tarin albarka, wadda muke da kyakkyawan zato za kuyi aiki bisa amana da gaskiya.
Hakazalika, Mai Martaba ya ja hankalinsu sosai duba da irin ƙalubalen dake gabansu dangane da aikin Allah da s**a ƙudiri niyyar yi, ya ce kada ku yarda ayi amfani daku domin zaluntar al’umma.
A ƙarshe Mai Martaba Sarki ya musu fatan alheri da sanya musu albarka a wannan gagarumin ayyuka nasu a faɗin Jihar Jigawa.
Sun sami tarba daga wajen ‘yan Majalissar sa daga cikinsu akwai Mai Girma Galadima, Waziri, Madaki, Sarkin Bai, Marafa, Sarkin Fada, Jakadan Sulhu, Magatakarda, Barwa da sauransu.
Allah ya taumaki Sarki, Allah ya ja Zamanin Sarki, Allah ya Jiƙan Baba Sarki ya ƙarawa Mai Babban Ɗaki Lafiya.
📸/✍️:
Copied from: Nasir Ibrahim, sNITP
Wazirin Tafarkin Dutse
Fadar Mai Martaba Sarki
Laraba, 21st January, 2025.