05/05/2026
KUNGIYAR DCPA TA ZIYARCI SAKATAREN KARAMAR HUKUMAR DUKKU
A yau Talata 5/5/2026 kungiyar ci gaban kasar Dukku, Dukku Community Progressive Association (DCPA) ta ziyarci Sakataren karamar hukumar Dukku Alh. Mustapha Bappayo domin sada zumunci, da tattauna muhimman batutuwa da s**a shafi ci gaban kasar Dukku.
Shugaban kungiyar Alh. Sambo Gorki ya mika sakon taya murna bisa samun mukamin Sakataren karamar hukuma, sannan ya jinjina masa bisa hakurin sa, da kyakkyawar mu'amalar sa da al'umma.
A karshe Gorki ya mika bukatar DCPA na neman hadin kansa ta fiskacin shawarwari, da yin aiki tare wajen ganin Dukku ta cigaba.
Sakataren karamar hukumar Dukku Alh. Mustapha Bappayo ya bayyana farin cikin sa bisa ziyarar da aka kawo masa, sannan ya yabi kokarin DCPA wajen shige da fice domin ganin Dukku ta cigaba.
Alh. Mustapha ya shawarci shugabannin DCPA dasu zama masu hakuri, da jajircewa a hidimar ayyukan kungiya.
Umar Babagoro Dukku
5/5/2026