Jigawa Youth Awareness and Mobilization in Society JYAMS

Jigawa Youth Awareness and Mobilization in Society JYAMS Awareness humanity in progress

14/02/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Abdulkareem Mamman, Mujahid Zaitawa, Kaka Chari Maloum Gana, Surajo Dahiru, Khadija Yargata, Alhajiumaru Betuwa, Abubakar Magaji, Asheer Muhammad Muhammad, Umar Ibrahim, Muhammad Badaru, Sani Adamu, Gaman Kanimare, It'z Shuaibu Isyaku, Lawal Garba Goronyo, Hassan Pkm, Tukur Muhammad, Nura Abdullahi, Umar Sani Kebbi, Dangaladiman Bebejin Katsina, Muhammed Sani Kuriga, Audu Rahman, Adamkanta Aji Ingima, Modu M Jalo Nganzai, Abdulrazak Musa Malal, Ashiru Abdullahi, Abubakar Mahuta, Kabiru Kabiru, Badamassi Yakouba, Bello Abubakar, Basiru Basiru, Sadiq Akowe, Ahamed Shehou, Alamin Umar, Bashar Sa'adu, Tijjani Isah, Adamu Muhammadu Adamu Muhammadu, Jamilu Lawal, Mohammed Musa, Baban Gayu Arewa, Sule Muhammad Doka, Dauda Musa, Yusif Salisu, Ibrahim Kalil, Ibrahim Lawan, Su Tarajo, Ïtz Égßåtî, Lawan Idris, Sahibi Aliyu, Abdullahi Musa, Yusufa Abbah

02/02/2026

Damuwarka tazama sirrinka Kar kazama mai yawan bayyana damuwar ga kowa domin wasu kullum burinsu suga damuwarka

boye damuwa a zuciya tabbas abune mai wahala ga wasu mutane Amma shine abu Mafi dacewa dan rikitar da wanda baya bukatar ganinka a cikin farin ciki

Damuwa halittace Marar kwatantuwa domin ba kowanna mutum bane yake iya biyeta Amma tabbas idan har ka iya boye damuwarka to hakan zai saukakama wajan baiwa wasu damar yima dariya a wannan duniyar

Idan damuwa tayi tsanani wasu lokuta mutum baya sanin lokacin da yake firtata ga mutane dan yasamu saukin radadin da yakeji na zuciyarsa

tabbas damuwa babban ciwone domin takansa a yanke jiki a fadi wasu lokutama har arasa rai

kayarda da kaddara ka yarda da samu da rashi kayar da cewar komai daga Allah ne Kuma shi yanufa da komai yafaru sannan ka ringa tuna cewar komai na duniya mai wucewane ita kanta duniyar kararriyace bare abin dake cikinta

Tabbas idan kayi hakan ko kazama mai yawan tunawa da hakan aduk lokacin da kashiga damuwa to tabbas zaka samu saukin radadi ko fadawa wani hali na damuwa

Bamayi danwani ba Kuma zamufara dan kaiba Baka kai muyi dan kaiba ba Kuma zaka sa muyi dan kaiba Wasa da dariya hakan fa...
30/01/2026

Bamayi danwani ba Kuma zamufara dan kaiba

Baka kai muyi dan kaiba ba Kuma zaka sa muyi dan kaiba

Wasa da dariya hakan fara'ane
Amma yawan yinsa gasu mutane yakan jawo raini

Kanajiran wani yayima to waye shi domin kuwa bai kaiba

Kana tsammani daka gareshi akan me bayan shima nema yake

Kajira wani yasamu kasamu akan wanna dalili bayan shima bashi zai bawa kansaba

Kanema a gurin Wanda yakeyi
Kanema a gurin da ba agori
Kanema agurin da baida iyaka
Kanema agurin Wanda baya tutiyar ni naima
Akanema agurin Wanda baya gajiya wajan bayarwa

Allah shine maiyin komai
Shine mai bayarwa ga Wanda yaso Kuma a lokacin da yaso

Ba ruwansa da matsayi ko cancanta idan har kana cikin Wanda zai yiwa to tabbas sai ya yima

Katashi ka nema Amma agurin Allah ba a gurin kowaba
Domin shine maiyi ba kowaba

Babu wani mutum da zai iya yima in ba Allah ba

Duniya mai cikike da abubbuwan ban mamaki kabiyeta ka halaka ka kita ka wahala shin to wai maye mafitar kenan da Kuma da...
28/01/2026

Duniya mai cikike da abubbuwan ban mamaki

kabiyeta ka halaka ka kita ka wahala

shin to wai maye mafitar kenan da Kuma dai daito da Samar da kwanciyar han Kali a cikinta

dole kazama mai wayo Kar kabari ta rudeka
kazama mai lissafi karkabari ta ringa lissafaka
kazama Kafi karfin zuciyarka dan Kar kabari ta rudeka
kazama mai yawan tuna da mutuwa ko dan zuciyarka ta rusuna dan Kar tayi tasiri a kanka
kazama mai juriya dan Kar wahalarta tasaka ka kauce
kar kayarda da yaudar da zatama da kyale kyalan dake cikin har tasa ka fada halaka

Duniya abar tsoroce sannan Kuma abar soce

kasota dai dai musali domin duk san da yayi yawa to tabbas akwai cutarwa a cikinsa

Ya Allah ka tsaremu da rudun duniya da abin da ke cikinta.

Jiya ta wuce yau Kuma muna cikinta gobe Kuma bamusan aya zatazoba Samu da rashi dukka na Allah ne hakuri juriya da kau d...
27/01/2026

Jiya ta wuce yau Kuma muna cikinta gobe Kuma bamusan aya zatazoba

Samu da rashi dukka na Allah ne hakuri juriya da kau da kai dan Samar da zaman lafiya hakan ba laifi bane

Kazama mai kokari wajan nema Amma Kar kazama mai dagiya wajan da katar da nasarar wani

Hassada mummun ciwone yi kokari ka yaki zuciyarka Kar kabarta tasa kayi asarar lokacinka wajan kokuwa da dakile nasarar wani

Abin dan zai faru da bawa rubutaccene daga min indillah kar kace zakayi hassada da hakan in Kuma kaki zaka wahala matuka

Yin hassada bata lokacine
Yin hassada asarar lokacine
Yin hassada rashin tawakaline
Sannan yin hassada yaki da abin da Allah ya kadarta akan bawan sane

Kowa kaga yasamu ba wayansabane yasa yasamu ba Kuma dan yafi kowa bane haka Allah yaso

Shiyasa yakeyi ga wanda yaso a lokaci da yaso

Ja da ikon Allah ko abin da Allah ya kadarta tabbas wahalace da sanya kai a cikin damuwa

Katashi kanema kai ma Allah zai baka rabonka
Kowa kagani dashi rabansane Allah ya bashi kaima naka zai zo yasameka a duk inda kake

Wayo da dabara ko zafin nema bayasa Allah yaba
Kyautace tasa ga Wanda yaso a lokacin da yaso

26/01/2026

ZAFIN NEMA

Tabbas zafin nema baya kawo samu Amma yana kare mutunci

Nema badare ba rana bashi kesa kayi arzikiba Amma tabbas yanayiwa talauci barazana

Yawan nemanka yakan rabautaka da abubbuwa da yawa da Kuma kare mutunci da kimarka gurin al'umma

Da acemaka Marar zuciya gara acema wancan Mayan neman kudine

Neman halak ko cikin ruwa ko iska cikin zafin rana ko sanyi sanin kimane da karawa kai daraja

Ba'a Allah wadai da mai fafutukar nema Amma ana Allah wadai da Marar zuciya

Nema bashine arzikiba Amma tabbas nema na kankaro daraja da kima K**a daga cikin gida har zuwa gurin al'umma

Mai nema yana tare da samu sannan mai nema asirinsa baya taba yayewa

Sanin asali da mutunci shine katashi kanema, kayi fada akan halinka dinka shine kacika jarumi ba karinga tada jijiyar wuya akan wani abuba

Da kajira abaka gara ajira kabayar
Da kasa ran za abaka gara asaran zaka bayar
Da acema gashi Kara kace gashi ko babu yawa
Da ace kai kake jira gara ace kai ake jira
Da acema baka da abinyi gara ace ma bashi da lokaci aje da wani
Da kayi barci dan baka dashi gara ka kasa barci dan baka da lokaci

Katashi kanema dare safe da yamma kayan nama baya kashe dan kura

**ZAFIN NEMA BAYA KAWO SAMU DOMIN ARZIKI NA ALLAH NE**

23/01/2026

Komai mai wucewane dan uwa kadaina damun kanka na sai ka mallaki abin da yafi karfinka

duk wani abu da zakayi fafutuka akansa da yawuce aljannarka dan uwa duk aikin banzane

Duniya da abin dake cikinta kyale kyale duk wani ado dake cikin tabbas idan ka biyesu to zakayi asarar gobanka

Babu abin dake cikin wannan rayuwa face rudu da yaudara dole sai kayi tunani sosai sannan Kafi karfin zuciyarka sannan zaka iya nasarar samun gobanka

Mutuwa takan zone lokacin da mutum bai shiryaba domin ba tambaya takeba bare kashirya kafin zuwanta

manta da dukkan wani abin kyale kyale da Kawa dake cikin wannan duniyar kai dai K**a Allah sannan kayi aiki tukuru dan neman lahirarka

yau tazo Koda kai ko bakai zatawuce Amma goban baka san aya zatazoba ba Kuma kasan da wanna irin abu zata zoba

ka kula sannan kayi taka tsantsan da rayuwa in Kuma kaki to tabbas zakayi asarar zuwanka duniya

Barkanmu Da Juma'a

wahala na zuwane lokacin kare mutunci da neman halak kai namijine Kar kaji tsoron wahala Dan gudu wasu suganka kana yint...
22/01/2026

wahala na zuwane lokacin kare mutunci da neman halak

kai namijine Kar kaji tsoron wahala Dan gudu wasu suganka kana yinta idan Kuma kaki to tabbas zaka zama abin dariya a gurinsu

ko Kuma kazama abin tambaya da zarar anrasa wani abu a unguwarku

bayan wuya sai Dadi duk kannin wani tsanani na tare da sauki

wahala takan zama ado da abin tarishi a gurin gwarzon namiji

ba a suna batare da an wahalaba duk Wanda kaga yazama wani to tabbas anji jiki

ka zama namiji mai jure wahala bamai tsorontaba

ka zama mai tunkar ta da daukarta a duk lokacin da tazoma domin alamar nasarace

wahala ba abar tsorobace domin tana wucewa Kuma tabbas bayan wuya sai dadi

21/01/2026

Wasu kullum burinsu suji laifinka

Wasu kullum fatansu suga faduwarka

Wasu kullum ihunsu suga gazawarka

Wasu kullum mafarkinsu suga kasawarka

Wasu bukatarsu kullum suga rashinka

Wasu kullum tunaninsu shine suganka cikin wahala

Ka manta dasu karufe idinka
Ka jajirce ka manta da maganarsu
Kayi aiki tukuru sannan ka Kalli abin dake gabanka
Kar kabari maganganunsu susanya ka nuna gazawarka agaresu

Ba'a samun nasara babu kalubale nasara bata zuwa batare da jarabawaba hassada kyashi bakin ciki matakin nasarane na rayuwa kamanta da masuyi ka cigaba dayin abin dake gabanka

Address

Kangire
Birnin-Kudu
2345

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jigawa Youth Awareness and Mobilization in Society JYAMS posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Jigawa Youth Awareness and Mobilization in Society JYAMS:

Share