Muryar Birnin Kudu

Muryar Birnin Kudu The Greatest Association of Birnin Kudu

10/04/2026

SANARWA TA MUSAMMAN!!!

Kwamitin Ilimi na Muryar Birnin Kudu na sanar da al’umma cewa, Muryar Birnin ta shirya bayar da horo kan yanda dalibai zasu rubuta JAMB domin samun nasara.

Ga duk daliban da ke sha'awar koyo daga mazabun Birnin Kudu, Kangire, Kiyako, Lafiya, Surko, da Worno zasu je GOVERNMENT GIRLS DAY SENIOR SECONDARY SCHOOL, BIRNIN KUDU (MASAMAWA) gobe Asabar 11/04/2026 daga karfe 9am zuwa abin da ya sawwaka.

Sauran 'yan mazabun Sundimina, Kantoga, Unguwar 'Ya, Kwangwara da Yalwandamai zasu halarta ranar Lahadi 12/04/2026 su ma daga karfe 9am zuwa abin da ya sawwaka.

___________
Kabiru Zubairu
A madadin Kwamitin

Ramadhan 1447 Day 3At Birnin Kudu:IFTAR: 6:34PMASSALATU: 5:30AM
20/02/2026

Ramadhan 1447 Day 3
At Birnin Kudu:
IFTAR: 6:34PM
ASSALATU: 5:30AM

Ramadhan 1447 Day 1At Birnin Kudu:IFTAR: 6:33PMFAJR: 5:31AM
18/02/2026

Ramadhan 1447 Day 1

At Birnin Kudu:
IFTAR: 6:33PM
FAJR: 5:31AM

20/01/2026

GIDAUNIYAR ILIMI TA MURYAR BIRNIN KUDU

Duba da muhimmanci da kuma bukatar da ake da ita, kuma kamar yanda Kwamitin Tarbiyya na Muryar Birnin Kudu da sauran wasu al'umma s**a bayar da shawara, Muryar Birnin Kudu ta samar da GIDAUNIYAR ILIMI.

Wannan gidauniya zata yi aiki domin tallafawa daliban asalin ƙaramar hukumarmu da makarantunmu da cibiyoyin iliminmu gwargwadon bukata da cancanta.

Wannan gidauniya zata kasance karkashin shugabancin MALAM HASSAN NAYAYA da sauran mambobi da zasu taya shi.

Akwai cikakkun tsare-tsaren yadda ayyukan bayar da tallafi da na neman tallafin suke wanda za a sanar nan ba da jimawa ba ga al'umma.

______________
Kabiru Zubairu Sufi
A madadin Kwamitin Riko
Muryar Birnin Kudu

28/12/2025

TARON WAYAR DA KAI KAN HIKIMOMIN BUNKASA KASUWANCI DA KARE JARI 2025

Salam,
Duba da yanda harkokin kasuwanci ke kasancewa da irin rugujewar jarin 'yan kasuwa da masu sana'o'i da ake yawan samu da ma batun karancin ciniki da samun ayyuka ga 'yan kasuwa da masu sana'o'inmu, MURYAR BIRNIN KUDU ta shirya taro na musamman kan magance wadannan matsaloli.

A wajen taron za a tattauna batutuwa kamar haka:
1. Tsara kasuwanci da dabarun bunkasawa.
2. Kyakkyawan tsarin sarrafa kudade da bayar da kariya ga jari.
3. Samarwa kai samfuri, tallatawa da kula da kwastomomi.
4. Hanyoyin samun tallafe-tallafe da bashin kasuwanci daga hukumomi da kungiyoyi masu temakawa.
5. Damarmakin iya fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje da kuma shigowa da su.
Akwai kwararru da hukumomi da aka gayyata don cimma nasarar abin da aka sa a gaba.

Domin kasancewa daya daga cikin _participants_, a turo bayanai kamar haka:
1. Cikakken Suna
2. Sana'a ko Kasuwanci
3. Sunan Wajen Sana'a ko Kasuwanci
4. Adireshin Wajen Sana'a ko Kasuwanci
5. Adireshin Wajen Zama
6. Shekarun da Aka Debe Ana Kasuwanci ko Sana'a
7. Lambar Waya da Email
Za a tura wadannan bayanai ta WhatsApp zuwa 08037872140 kuma za a rufe karbar bayanan ranar Litinin 29/12/2025 da karfe 6 na yamma.

Za a gudanar da wannan taro ne ranar Laraba 31/12/2025 a Da'u Aliyu Hall da karfe 10am zuwa 2pm.

*Burinmu shine samar da Birnin Kudu mai bunkasar tattalin arziki da wadatar ayyukan yi.*

____________________
Kabiru Zubairu Birnin Kudu
Shugaban Kwamitin Tsare-Tsare

ZIYARA GA BARR. ALI SA'ADU DA HON. ROSSIA ci gaba da ziyarar neman goyon baya da samun hadin kai don samarwa Karamar Huk...
02/12/2025

ZIYARA GA BARR. ALI SA'ADU DA HON. ROSSI

A ci gaba da ziyarar neman goyon baya da samun hadin kai don samarwa Karamar Hukumar Birnin Kudu ingantaccen cigaba, Kwamitin Riko na Muryar Birnin Kudu a yau Talata 02/12/2025 ya ziyarci tshohon Gwamnan Jigawa, Barrister Ali Sa'adu Birnin Kudu da Dan Majalisar Jiha mai Wakiltar Birnin Kudu, Hon. Muhd Kabir Ibrahim Rossi a gidajensu da ke Kano.

An tattauna muhimman batutuwa da s**a shafi hanyoyin samarwa karamar hukumarmu cigaban da take bukata.

Dukkan jagororin da aka ziyarta, sun nuna farincikinsu da yin alkawarin cigaba da bayar da gudunmawa wajen inganta cigaban al'ummarmu.

__________________
Kabiru Zubairu
A madadin Kwamitin Riko

NEW BKD MICROFINANCE BANK JOB ADVERTISEMENT
02/12/2025

NEW BKD MICROFINANCE BANK JOB ADVERTISEMENT

Salam,A jiya Lahadi 30/11/2025, Shugabancin Muryar Birnin Kudu ya kai ziyarar zumunci da fahimtar juna wajen Shugaban Ka...
01/12/2025

Salam,

A jiya Lahadi 30/11/2025, Shugabancin Muryar Birnin Kudu ya kai ziyarar zumunci da fahimtar juna wajen Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Dr. Muhammad Uba.

An tattauna batutuwan da s**a shafi ci gaban ƙaramar hukumarmu kamar bangaren ruwan sha, tsaro da sauransu. Inda a bangaren tsaro, Shugaban Karamar Hukuma yai alkawarin dawo da 'yan sintiri domin magance sace-sace da sauran ayyukan ɓata-gari.

Dr. Muhammad Uba ya taya Kwamitin Riko na Murya murna tare da alkawarin ba shi hadin kai don cimma manufar da aka sa a gab.

Shugaban Kwamitin Rikon, Alhaji Ahmad Sa'id Kangire, a madadin Muryar Birnin Kudu da sauran al'umma, ya godewa Shugaban Karamar Hukuma bisa nuna jajircewarsa wajen magance matsalolin ƙaramar hukuma.

Ya kuma yi alkawarin cewa, Muryar Birnin zata ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen ganin an samu ci gaba a fannoni daban-daban na rayuwar al'ummar Birnin Kudu.

_______________
Kabiru Zubairu
Mai Kula da Shafukan Sada Zumunta na Muryar Birnin Kudu

Salamun Alaikum,A jiya Asabar 29/11/2025 ne Kwamitin Riko na Muryar Birnin Kudu ya gana da dukkan wakilcin kungiyoyin ci...
30/11/2025

Salamun Alaikum,

A jiya Asabar 29/11/2025 ne Kwamitin Riko na Muryar Birnin Kudu ya gana da dukkan wakilcin kungiyoyin ci gaban karamar hukumar Birnin Kudu daga dukkan mazabu 11 don ƙarfafa alaka da neman yin aiki tare don samun cikakkiyar nasara.

An tattauna sosai an kuma ba wa juna shawara kan yanda al'amura ya kamata su kasance don samun cikakkiyar nasarar samawa karamar hukumarmu ci gaban da ake bukata.

Ga wasu daga hotunan da aka dauka wajen taron, wanda aka yi a Da'u Aliyu Hall, kuma ya samu halartar Mai Girma Sarkin Kudu, Shugaban Kwamitin Amintattu na Muryar Birnin Kudu, Alhaji Hussaini Hassan Jibrin.

MIKA MULKI GA KWAMITIN RIKON KWARYAA yau Lahadi 23/11/2025 Kwamitin Zartarwa wanda ya sauka ya mika mulkin Muryar Birnin...
23/11/2025

MIKA MULKI GA KWAMITIN RIKON KWARYA

A yau Lahadi 23/11/2025 Kwamitin Zartarwa wanda ya sauka ya mika mulkin Muryar Birnin Kudu ga Kwamitin Rikon Ƙwarya wanda zai daidaita tafiyar al'amuran Muryar Birnin Kudu tare da samar da sabbin shugabanni a cikin watanni 6 masu zuwa.

Shugabannin da s**a sauka sune:
1. Alhaji Balarabe Sa'id Jarma (Shugaba)
2. Alhaji Idris Ibrahim Urban (Mataimakin Shugaba)
3. Malam Dauda Mu'azu (Sakatare)
4. Alhaji Ibrahim Isyaku (Mataimakin Sakatare)
5. Hajiya Jummai Bala (Ma'aji)
6. Malam Auwal Yusuf Isah Kiyako (Sakataren Kudi)
7. Malam Kabiru Zubairu (Sakataren Yada Labarai)
8. Alhaji Yahaya Uba Kafingana (Mataimakin Sakataren Yada Labarai)
9. Alhaji Basiru Yusuf Extra (Sakataren Shirye-Shirye)
10. Malam Kabiru Yau (Mataimakin Sakataren Shirye-Shirye)
11. Barr. Abdulkadir Lurwanu Fanini (Mai ba da Shawara kan Harkokin Shari’a)
12. Hajiya Aisha Ilyasu Surko (Wakiliyar Mata)
13. Alhaji Shehu Saleh (Mai Binciken Kudi)
14. Engr. Sule Sani (Mai Kula da Walwala)

Ƴan Kwamitin Rikon Sune:
1. Alhaji Ahmed Said Kangire (Shugaba)
2. Dr. Hadi Mohammed (Sakatare)
3. Alhaji Abdullahi Kawo (Ma'aji)
4. Alhaji Suleiman Adamu (Mamba)
5. Dr. Abubakar Uba (Mamba)
6. Alhaji Abdullahi Mohammed Matawalle (Mamba)
7. Hajiya Uwani Jafaru (Mamba)

Tsohon Kwamitin Zartarwa ya mika dukkan bayanai da kadarorin kungiya ga sabon kwamitin riko. An tattauna tare da bayar da shawarwari ga sabon kwamitin an kuma dauki hotuna tare da taya juna murna.

Bayan haka, Kwamitin Rikon ya kai ziyara ga Mai Girma Sarkin Kudu, Shugaban Kwamitin Amintattu na Murya, Alhaji Hussaini Hassan Jibrin. Mai Girma Sarki ya taya murna tare da yin alkawarin ci gaba da marawa ayyukan Muryar Birnin Kudu baya da wucewa gaba don a samar da ci gaban da ake bukata a al'ummarmu.

_______________
Kabiru Zubairu
Mai Kula da Shafukan Sa da Zumunta na Muryar Birnin Kudu

16/11/2025

SAUYIN SHUGABANCIN MURYA

Salamun Alaikum,

Biyo bayan uzurai da s**a yi wa da dama daga cikin 'yan Kwamitin Zartarwa na Muryar Birnin Kudu da yanayi na ayyuka wadanda s**a hana tafiyar al'amuran Murya yanda ya kamata, yau Lahadi 16/11/2025, Kwamitin Gudanarwa (CWC), kamar yanda Kudin Tsarin Mulkin Muryar Birnin Kudu ya ba shi dama, ya sauke dukkan 'yan Kwamitin Zartarwa mai mutum 14 tare da nada Kwamitin Zartarwa na riko wanda zai kula da ayyukan zartarwa tare da samar da sabbin shugabanni cikin watanni uku zuwa shida masu zuwa.

Mambobin 'yan Kwamitin Rikon sune:
1. Alhaji Ahmad Sa'idu Kangire
2. Alhaji Sule Adamu (Binot)
3. Dr. Hadi Muhammad
4. Dr. Abubakar Uba
5. Alhaji Abdullahi Kawo
6. Alhaji Abdullahi Mohammed (Matawalle)
7. Hajiya Uwani Jafaru (former PS)

Daga yau Lahadi 16/11/2025, dukkan al'amuran tafiyar da Murya ya koma hannunsu. Da fatan zasu samu dukkan hadin kan da ya dace domin tabbatar da Muryar Birnin Kudu mai inganci wadda zata jagoranci samar da ayyukan ci gaba a karamar hukumarmu.

_______________
Kabiru Zubairu
Sakataren Yada Labarai,
Mai Barin Gado

Address

Birnin-Kudu

Telephone

+2348037872140

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muryar Birnin Kudu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Muryar Birnin Kudu:

Share