02/10/2026
JAWABIN CIKAR NIGERIA SHEKARU 66
Daga: Jagoran Kungiyar JIBWIS Nigeria, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau
Bismillahir Rahmanir Rahim.
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.
'Yan uwa Musulmi, 'yan uwa 'yan kasa baki daya.
A yau, Nigeria ta cika shekaru 66 da samun 'yancin kai. Shekaru 66 na tarihi, na darussa, na kalubale, da kuma ni'imomi marasa adadi da Allah Ya yi mana a wannan kasa tamu. Wannan rana ba rana ce ta biki kawai ba, rana ce ta yin tunani da kuma muhasaba.
A wannan rana mai muhimmanci, ina so in gabatar da wannan nasiha da jan hankali a gare mu baki daya.
NA DAYA: JAN HANKALI GA SHUGABANNIN MU
Ya ku shugabannin mu, tun daga matakin kasa har zuwa jihohi da kananan hukumomi, ku sani cewa shugabanci amanar Allah ce kuma Allah zai tambaye ku a kansa gobe Kiyama.
Nigeria ba ta da matsalar albarkatu, tana da matsalar shugabanci na gari. Ku ji tsoron Allah a cikin al'amuran da aka danka muku.
Allah Madaukakin Sarki Yana cewa a cikin Al-Qur'ani mai girma:
إِنَّ اللَّهَ يَأْمُرُكُمْ أَن تُؤَدُّوا الْأَمَانَاتِ إِلَىٰ أَهْلِهَا وَإِذَا حَكَمْتُم بَيْنَ النَّاسِ أَن تَحْكُمُوا بِالْعَدْلِ
“Lallai Allah Yana umartar ku da ku bayar da amanoni ga masu su, kuma idan kuka yi hukunci a tsakanin mutane, ku yi hukunci da adalci.” [Suratun Nisa’i: 58]
Shugabanci ba gata ba ne, nauyi ne. Adalci, rikon amana, da tausayawa talakawa shi ne zai fitar da mu daga halin da muke ciki. Ku rike amana ku tsaya wajen kare Addinin Allah, rayuka da dukiyan al umma, ku sanya ido matuka a kan tsaro, ba hasara cikin duk abinda aka kashe don a Samu zaman lafiya.
NA BIYU: JAN HANKALI GA TALAKAWA
Ya ku 'yan uwa talakawa, ku sani cewa gyaran kasa baya farawa daga sama kadai, yana farawa daga kowane gida.
Matsalar tsaro, rashin zaman lafiya, da talaucin da muke ciki, duk suna da alaka da nisantar mu daga Allah da kuma yadda muke mu'amala da juna. Mu gyara halayen mu, mu dena hassada, yaudara, cin amana, da shiga kungiyoyin da suke kawo fitinaنَّ