30/09/2026
Jami’ar Covenant, Jami’ar Ibadan da Jami’ar Lagos sun kasance jami’o’in Najeriya mafi matsayi a sabon jadawalin Times Higher Education World University Rankings na shekarar 2027.
Dukkan jami’o’in uku an sanya su a matsayi na 801–1000 a duniya, yayin da Najeriya ta samu jami’o’i 29 da aka sanya a jadawalin bana, daga 24 da aka samu a shekarar 2026.
A cewar rahoton, Jami’ar Covenant ta dawo matsayi na farko a tsakanin jami’o’in Najeriya, bayan da Jami’ar Ibadan da Jami’ar Lagos s**a kasance a kan gaba a shekarar 2026. Sai dai a sabon jadawalin, jami’o’in uku suna cikin rukuni guda na 801–1000 a duniya.
Bayan su akwai Jami’ar Ahmadu Bello da Jami’ar Bayero, wadanda suke cikin rukuni na 1001–1200 a duniya. Jami’ar Landmark da Jami’ar Ilorin ma suna cikin wannan rukuni.
A bana, jami’o’in Najeriya biyar sun fara bayyana a jadawalin, wadanda s**a hada da Osun State University, University of Maiduguri, Olabisi Onabanjo University, Kwara State University da Michael Okpara University of Agriculture, Umudike.
Times Higher Education ta ce jadawalin na 2027 ya kunshi jami’o’i 2,297 daga kasashe da yankuna 118, inda ake duba fannoni biyar da s**a hada da koyarwa, muhalli da ingancin bincike, hangen duniya da kuma alakar jami’a da masana’antu.
A bangaren jami’o’in Najeriya da ba su samu matsayi ba, Abubakar Tafawa Balewa University da wasu jami’o’i 32 an sanya su cikin rukunin “reporter institutions”, wato jami’o’in da s**a gabatar da bayanai amma ba su cika sharuddan da ake bukata domin samun matsayi ba.