Team Kwanar Gari-KG

Call Directions Contact the organization

Team Kwanar Gari-KG Youths Teaming Group

KUNGIYAR TEAM KG ALIERO TA BARRANTA KANTA DAGA GOYON BAYAN KAURAN GWANDU A KARO NA BIYUA madadin ƙungiyar matasan TEAM K...
03/07/2026

KUNGIYAR TEAM KG ALIERO TA BARRANTA KANTA DAGA GOYON BAYAN KAURAN GWANDU A KARO NA BIYU

A madadin ƙungiyar matasan TEAM KG Aliero, muna masu barranta kanmu daga duk wata tafiya dake da alaƙa da goyon bayan zaɓen His Excellency Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) a karo na biyu.

Wannan hukunci ya biyo baya ne bayan ƙungiyar ta zauna ita da ƴaƴanta, ta yi nazari da bincike kan gano shin wane cigaba ne gwamnatin Kauran Gwandu ta kawo wa wannan ƙaramar hukuma mai albarka, ko ta kawo wa matasan Aliero?

Inda ƙungiyar ta kai ƙarshen zaman nata ba tare da ta iya kawo asalin tantagaryar cigaban da za a iya kallo da idanun basira a matsayin cigaban da gwamnatin nan ta kawo a Aliero ba.

Ƙungiyar ta matasa masu kishin cigaban al'ummarsu, ta janye duk wani goyon bayanta ga gwamnatin Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu), tare da kira ga dukkan ƴaƴanta na ko'ina da su cire hannayensu cikin duk wata tafiya da ke da alaƙa da goyon bayan His Excellency Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) a karo na biyu.

NB: Zuwa yanzu ƙungiya ba ta yanke hukunci a kan wanda za ta goyawa baya ba. Don haka ƙungiya na kira ga dukkan ƴaƴanta da su kasance masu biyayya ga uwar ƙungiya kamar yadda s**a saba kafin su ji umurni na gaba. Mun gode!

Signed

Thu, 2nd July, 2026.

Address

Near Corpers Lodge, Kwanar Gari
Aliero

Telephone

+2348034731684

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Team Kwanar Gari-KG posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Team Kwanar Gari-KG:

Shortcuts

Share