01/09/2025
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ðŸ˜
Yau 30/08/2025 Barayi Bandits sun je yankin Dogonruwa, Tashar Mangoro, Buturkai ( Makera Ward Dutsin-ma Local Government) sun harbi Mutum 3 sun Kashe 1 sun Dauki Shanu 4 kowa ne zai iya kai 2m qila.
Jama'a Dogonruwa da Tashar Mangoro suna bakin kokarin su kusa 1hr suna bata Kashi amma saboda Makamai ba Daya ba, sai da s**a tafi da Shanu duka.
Tsakani ga Barayin sun ci karfin mutanen Dogonruwa da Tashar Mangoro tun da ga shi sunzo gab da Gadar Zobe Dam sun kwashi Shanu.
Babban gurin su ketara T**i matukar ba a kai ma Mutanen Dogonruwa da Tashar Mangoro Daukin Jami'an Tsaro ba, mutanen yankin sun dade suna Jarumta amma hukumomi sun gaza temaka masu da Jami'an Tsaro kamar yadda s**a taimaki yankin KUKI.
Tabbas Makera Ward gabas da yammanta baki daya Bandits sun kusa cimmata.
Allah ya bamu mafitah da mafitarsa Amin 🤲ðŸ˜
Daga shafin Bashir Dogonruwa