27/09/2026
Wani Matashi Ya Yi Ajalin Mahaifinsa Mai Shekaru 80 A Katsina
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta sanar da cafke wani matashi mai suna Sada Tambai, mai shekaru 27, bisa zargin hannu a mutuwar mahaifinsa, Adamu Tambai, mai shekaru 80, a ƙauyen Mundadu da ke Ƙaramar Hukumar Bindawa ta jihar Katsina.
A cewar rundunar ’yan sandan, lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Satumba, 2026, inda aka samu dattijon kwance ba ya motsi a wajen gidansa.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq-Aliyu, ya bayyana cewa an garzaya da dattijon zuwa asibiti domin samun agajin gaggawa, amma daga bisani likita ya tabbatar da cewa ya rasu.
Bayan gudanar da binciken farko kan lamarin, ’yan sanda sun ce sun samu nasarar cafke ɗan marigayin, Sada Tambai, wanda ake zargi da hannu a mutuwar mahaifinsa.
Rundunar ta ce yayin tambayoyi, wanda ake zargin ya bayyana cewa ya samu saɓani da mahaifinsa, inda ake zargin ya buga shi a kai da sanda, abin da ake zargin ya jawo mummunan rauni da kuma mutuwarsa.
Sai dai, rundunar ’yan sandan ta jaddada cewa bincike kan lamarin yana ci gaba da gudana domin gano cikakken abin da ya faru.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina ya kuma bayar da umarnin tura lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) domin gudanar da cikakken bincike.
Rundunar ta ce bayan kammala bincike, za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin ya fuskanci shari’a bisa tanadin doka.