18/09/2026
A cikin Musulunci, yarda da cewa Annabi Muhammadu (S.A.W) shi ne cikon dukkan annabawa kuma babu wani annabi a bayansa yana daya daga cikin ginshiƙai masu muhimmanci na aƙida da Imani da Annabawa.
Annabi (S.A.W) ya yi bayani dalla-dalla a cikin hadisansa domin jaddada wannan gaskiya:
Annabi (S.A.W) ya bayyana kansa da misalin gida mai matukar kyau wanda aka kammala gina shi, amma aka bar gurbi guda daya na bulo. Mutane na sha'awar gidan amma suna cew @ "Me ya sa ba a sa wannan bulon ba?" Sai Annabi (S.A.W) yace: "Aini ne wannan bulon, kuma ni ne cikon annabawa." (Bukhari da Muslim)
Dawateislami Trust Nigeria