22/09/2026
Labarin yaron da mahaifinsa ya cire shi daga makarantar boko domin ya haddace Alƙur'ani
Mahaifin yaron yace:
“Wannan ɗan autana ne, Ubayyu. Na cire shi tare da ƴan uwansa daga makarantar boko na tsawon shekara guda, domin na saka su a makarantar haddar Alƙur’ani, da fatan za su samu damar haddace Littafin Allah.
Mahaifinsa ya cigaba da cewa “A makon da ya gabata, na samu baƙon wani malami. Yayin da muke cikin tattaunawa, sai Ubayyu ya shigo, ya tambayi Malamin:
“Ta yaya ka yi hadda?”
Tambayar tasa ta nuna yadda tunaninsa ya fara karkata ga wannan babbar tafiya ta haddar Alƙur’ani.
Kafin ya fara, Ubayyu yana kallon hadda Alƙur’ani a matsayin abu mai sauƙi. Amma yanzu, da ya fara fuskantar aikin da gaske, ya fahimci cewa akwai ƙoƙari, juriya, maimaitawa da jajircewa a gabansa.
Muna roƙon Allah Ya sauƙaƙa masa wannan tafiya, Ya sa Alƙur’ani ya zauna daram a zuciyarsa, ya zama haske a rayuwarsa, tare da ƴaƴansa da sauran ƴan uwansa.