18/06/2026
SANARWAR!! SANARWA!!!
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh.
Kungiyar Daliban Jihar Kano mazauna Masar na sanar da daukacin mambobinta cewa, bisa la’akari da bukatar inganta tsarin shugabanci da tabbatar da sahihin zabe cikin adalci da gaskiya, an kafa Kwamitin Zabe na musamman domin gudanar da zaben kungiyar.
An dorawa wannan kwamiti alhakin tsara jadawalin zabe, karbar ‘yan takara, kula da dukkan matakan zabe, da tabbatar da cewa an gudanar da zabe cikin gaskiya, tsari, da bin dokokin kungiyar.
SUNAYEN KWAMITIN ZABEN SUNE KAMAR HAKA.
Sunayen kwamatin zaɓe:
Chairman
1- Malam Mukhtar Abdulmuminu (Jakara)
Mataimakin Shugaba
2- Malam Fasihullissan Tijjani.
Secretary
Malam Ismail Yushau (Attaysir.)
Mataimakin Sakatare
4- Malam Aliyu A. Adam (Gwammaja)
MA'AJIYI
5- Malam Aminu Ibrahim Muhammad.
Ma’ajin
(P.R.O)
6- Malam Saifullahi Lawan (Gwangwazo)
Don haka, muna kira ga daukacin mambobi da su ba wannan kwamiti cikakken hadin kai, tare da mutunta dukkan ka’idoji da sharuddan da za su gindaya domin nasarar wannan aiki mai muhimmanci.
Allah ya bada sa’a, ya kuma sa ayishi lafiya agama lafiya.
SANARWAR🎙️: General Secretary Aminu Nasir
Date: 14/6/2026