01/01/2026
January 1 2026.
BARKA DA SABUWAR SHEKARA.
A madadin Ƙungiyar Ɗaliban Jihar Kaduna a Masar, muna taya dukkan ɗaliban Jihar Kaduna murnar shigowar sabuwar shekara, tare da miƙa sakon fatan alheri ga dukkan ɗaliban Najeriya baki ɗaya. Muna roƙon Allah Ya sanya wannan shekara ta kasance mai albarka, cike da nasarar karatu, lafiya, kwanciyar hankali, da cigaba ga kowa.
Yayin da muke shiga wannan sabuwar shekara, muna kira ga kowane ɗalibin Najeriya da ya kasance cikin haɗin kai, zumunci, da kishin ƙasa. Ƙarfimmu tana cikin kasancewa tare, ba tare da la’akari da bambancin jihohi, kabilu, ko akidu ba, cikin girmamawa da ɗaukar alhaki na bai ɗaya. Ku tuna cewa kowane ɗalibin Najeriya a Masar jakada ne na ƙasarmu, Najeriya. Don haka, halayyarmu, maganganunmu, da ayyukanmu suna da matuƙar muhimmanci. Mu kasance masu bin doka, masu tarbiyya, kuma abin koyi a kowane lokaci.
Haka kuma, muna jaddada muhimmancin sabunta IQAMA (residence permit) a kan lokaci. Batun Iqama ba zaɓi ba ne, abu ne mai matuƙar muhimmanci. Ɗaliban da har yanzu ba su sabunta Iqaman su ba ana shawartarsu da su ɗauki wannan lamari da muhimmanci ba tare da jinkiri ba. A halin yanzu, irin waɗannan ɗalibai su rage yawo ba tare da dalili ba, su guji wuraren da ake yawan kamawa, su kuma kasance masu taka tsantsan har sai an kammala daidaita matsayinsu.
Yayin da jarrabawar zangon farko ke farawa, muna yi wa dukkan ɗalibai fatan alheri da nasara. Ku yi shiri sosai, ku mai da hankali, ku kuma ba da iyakar ƙoƙarinku. karatunku amana ce gare ku, ga iyayenku, da kuma ƙasarku.
A ƙarshe, muna sake yi muku barka da sabuwar shekara. Allah Ya sanya wannan shekara ta kasance ta haɗin kai, ɗaukar nauyi, da manyan nasarori.
Sa hannu:
Zakariyyah Zaria
Secretary General KADSSUE
🎙: Abdulkarim Shehu Abbas
PRO KADSSUE