25/12/2019
HUKUNCIN GAISHE DA
KAFIRI A RANAR IDIN
SU.
Ibnul Qayyim yace:-
ﻭﺃﻣﺎ ﺍﻟﺘﻬﻨﺌﺔ ﺑﺸﻌﺎﺋﺮ ﺍﻟﻜﻔﺮ
ﺍﻟﻤﺨﺘﺼﺔ ﺑﻬﻢ، ﻓﺤﺮﺍﻡ ﺑﺎﻻﺗﻔﺎﻕ!
ﻣﺜﻞ ﺃﻥ ﻳﻬﻨﺌﻬﻢ ﺑﺄﻋﻴﺎﺩﻫﻢ
ﻭﺻﻮﻣﻬﻢ، ﻓﻴﻘﻮﻝ: ﻋﻴﺪ ﻣﺒﺎﺭﻙ
ﻋﻠﻴﻚ، ﺃﻭ ﺗﻬﻨﺄ ﺑﻬﺬﺍ ﺍﻟﻌﻴﺪ، ﻭﻧﺤﻮﻩ،
ﻓﻬﺬﺍ ﺇﻥ ﺳﻠﻢ ﻗﺎﺋﻠﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﻜﻔﺮ،
ﻓﻬﻮ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺤﺮﻣﺎﺕ، ﻭﻫﻮ ﺑﻤﻨﺰﻟﺔ
ﺃﻥ ﻳﻬﻨﺌﻪ ﺑﺴﺠﻮﺩﻩ ﻟﻠﺼﻠﻴﺐ، ﺑﻞ
ﺫﻟﻚ ﺃﻋﻈﻢ ﺇﺛﻤﺎ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺃﺷﺪ
ﻣﻘﺘﺎ ﻣﻦ ﺍﻟﺘﻬﻨﺌﺔ ﺑﺸﺮﺏ ﺍﻟﺨﻤﺮ
ﻭﻗﺘﻞ ﺍﻟﻨﻔﺲ ﻭﺍﺭﺗﻜﺎﺏ ﺍﻟﻔﺮﺝ
ﺍﻟﺤﺮﺍﻡ ﻭﻧﺤﻮﻩ .
"1/441 "ﺃﺣﻜﺎﻡ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺬﻣﺔ.
Amma yin gaisuwa da
wasu alamu na kafirci
wanda ya kebanci su
(Nasara ko wasu
nau'ukan kafirai) to,
wannan HARAMUN NE
da ittifakin musulmi
akan haka.
Misali: Ya gaishe su sbd
idin su da azumin su
kamar yace: HAPPY
CHRISTMASS da
lafuzza makamantan
haka, to mafadin
wannan maganar idan
ya KUBUTA DAGA
KAFIRCI to, lalle shi
yana daga abubuwa da
aka haramta. Kuma shi
yana matsayin kamar
wanda ya gaishe shi ne
sbd sujudar sa ga Kross,
a gaskiya zunubin ma
yafi girma sama da
tayasu murna akan shan
giya da kisan kai da zina
da makamantansu cikin
abubuwan da aka
haramta
Abin lura:
1- Gaishe da kafiri
saboda bikin idin su
wannan haramun ne kai
tsaye, gaya mishi IDUKA
MUBARAKUN ko
HAPPY CHRISTMASS
ko wata kalma ta
gaisuwa duka haramun
ne.
Wanda ya gaishe da
kafiri a ranar Idin su to
IDAN YA KUBUTA DAGA
KAFIRCI TO BA ZAI
KUBUTA DAGA AIKATA
BABBAN ZUNUBI BA.
Gaishe da kafiri a ranar
bikin idin su zunubin
haka yafi girma fiye da
zunubin shan giya da
kisan kai da sauran
kaba'irai.
ALLAH ya shiryar damu
tafarkin tsira.
Dr. Kabir Asgar