06/09/2025
Muna mika ta'aziya a magazine Sauzar Academy Jen
Innā lillāhi wa innā ilayhi rājiʿūn.
Inna lillāhi mā akhaza wa lahu mā aʿṭā, wa kullu shay’in ʿindahu bi-ajalin musamman.
Jikin jimami da mika al'amari ga ubangiji muke sanar da rasuwar ɗan’uwanmu Sadik Ibrahim Mashall jen, wanda aka fi sani da Sadik Haske.
Bisa ga labarin da muka samu, ya raka bappansa Bakari domin sasanta rikici kan barna da shanu suka yi a gonar wani. A yayin wannan tattaunawa cece-kuce ya tashi tsakaninsu, inda mai gonar ya fara zagin bappan nasa. Sadik ya yi magana don kare bappansa, sai wani ya kai masa hari da mashi a gefen zuciya. Duk da cewa an garzaya da shi zuwa asibitin Jen, kafin a sami damar yi masa wani taimako, Allah (SWT) Ya karɓi rayuwarsa.
Allah Ya gafarta masa, Ya rahama masa, Ya sanya kabarinsa ya zama lambun Aljanna. Allah kuma Ya ba iyalansa, ‘yan uwansa da abokansa haƙuri da juriyar wannan babban rashi.
Source :
Anna's Harisu Dogo Jen