21/10/2022
ALHAMDULILLAH KAWO YANZU AN SAMU DUBU ARBA'IN DA BAKWAI 47k A CHIKIN 281K
sunan sa Malam Musa Muhammad , yana Zaune a UNGUWAR DADIN KOWA LAYIN MALAM ARI GISHUWA DOGO NINI WARD POTISKUM.
Tela ne mai karamin karfi, Allah ya jarrabeshi da jinya kusan shekara uku yana fama, wanda a halin yanzu baya iya tashi, komai sai ammasa, kwanakin baya mun nema masa taimako fisabilIahi a gurin al'umma domin kaishi asibiti, a wancan lokacin mun kaishi asibiti, anyi gwaje gwaje, wanda aka kasa gano menene ke damun sa, daga baya sai wasu kuraje s**a bayyana ajikin sa, muka sake komawa asibiti akayi gwaje gwaje sai aka gano yana dauke da UTI, da kuma Ulcer, bayan wannan gwajin, ya kwana biyu a asibiti yana jinya, gashi yana da mace tare da yara, komai nasa ya kare saboda jinya.
Acikin kwana kinnan mun kaishi teaching Hospital Damaturu, anyi gwaje gwaje, namma ba'a gano komai ba sai wannan infection din dake jikin sa, anyi har Urine MCS, EUCR, andora shi kan magani, amma kwata kwata ciwon baya jin magani domin maganin ya saba da jikinsa.
Shine aka bamu shawara cewa akwai wani magani na China wanda ake amfani dashi a fannin abun da ya shafi infection, kuma cikin ikon Allah ana dacewa.
Shine muka karbi shawara cewa zamu gwada yin maganin ciwon daya bayya ajikinsa.
An rubuta mana magani kala hudu kamar haka:
✓ Raishi,
✓ Golden Hypher,
✓ Cleanser,
✓ Gastriport.
Mun sayi wayannan magani naira dubu hamsin da shida da dari uku 56K
Bayan amfani da wayannan magani na tsawon sati biyu, cikin ikon Allah sai jikin malam Musa ya nuna alamar samun sauki sosai, gashi kuma maganin ya kare, kuma anaso ayi amfani da maganin na tsawon wata uku 56,300
A yanzu haka, muna neman wannan kudi dubu dari biyu da tamanin da daya, da dari biyar ( #281,500)
Muna neman fisabilillahi a gurin al'umma komai kankantarsu domin saya mar wayannan maganin, wanda kuma yana da daman da zai saya mana ga hoto nan a qasa
ASUSUN BADA TALLAFI
UBA
2246396901
Tukur Muhammad
Domin Karin bayani: 08146304379