Makuku Youth Development Association - MYDA

Makuku Youth Development Association - MYDA This is an official page of makuku youth, whatever is posted from this page is highly official

20/11/2025

Muna mika ta’aziyya ta musamman ga iyalan Marigayi Malam Hassan Makuku, Mataimakin Shugaban Makarantar GGCSS Maga, wanda aka kashe ta hanyar kisa mara imani. Hakika wannan babban rashi ne ga iyalansa, al’ummar Makuku, da dukkanmu. Allah Ya jikansa, Ya ba iyalai hakuri da juriya.

Haka kuma muna rokon Allah Ya tsare yaranmu dalibai 25 da aka sace, Ya dawo da su cikin koshin lafiya.

A madadin Makuku Youth Development Association (MYDA), muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jiha da su dauki matakai masu zuwa:
1. A tabbatar da ceto daliban da aka sace cikin gaggawa da lafiya.
2. A karfafa tsaro a fadin jihar, musamman a hanyoyin fita da shigowa, domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
3. A tabbatar cewa al’ummar Makuku sun samu kulawa, jaje, da dukkan taimakon da ya dace, domin wannan lamari ya girgiza mu matuka.

Allah Ya kawo mana zaman lafiya, Ya karemu daga dukkan sharri. Ameen.

Address

Makuku Town
Zuru
860101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Makuku Youth Development Association - MYDA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share