15/09/2026
Daga Aliyu Abdulrahman
An yi kira ga matasa su rungumi sana’o’i domin dogaro da kai
An yi kira ga matasa da su rungumi koyon sana’o’i domin dogaro da kansu don kauce wa zaman kashe wando.
Injiniya Abubakar Yakubu Nepa ne ya yi kiran yayin wani bikin kammala koyon sana’o’i da Shafa’u Rahma Foundation ta shirya a Unguwar Fatika da ke cikin birnin Zaria.
Ya ce koyon sana’a na taimakawa matasa wajen dogaro da kai, tare da ba su damar samun abin yi da kuma taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.
A nasa jawabin, Ambasada Yusuf Jibrin Barayan Sadaukin Zazzau ya yabawa shugaban gidauniyar Shafa’u Rahma Hajiya Shafa’atu Barau bisa kokarinta na horar da matasa Maza da Mata sana’a.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta taimaka wajen samar da kayan aiki da kuma tallafawa matasa domin su samu damar amfani da sana’o’in da s**a koya wajen samun abin dogaro da kai
Tunda Farko, shugabar kungiyar ta Shafa’u Rahma, Hajiya Shafi’atu Barau, ta nuna jin dadin ta bisa samun nasarar daukan nauyin yaran talakawa, ta kuma koya masu abinyi, a cikin aljihunta bata tare da karban ko sisin kwabo ba
Barau Kazalika ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da gwamnati da su kara kokarin tallafawa shirye-shiryen da ke samar da sana’o’i ga matasa,wanda a cewar ta hakan zai taimaka wajen rage zaman kashe wando da kuma hana yara aiyukan da basu kamata ba.
Wasu daga cikin daliban Umar Hafiz Ibrahim, da s**a kammala horon sana’a, ya ce koyon sana’ar ya taimaka masa wajen samun kwarewar da zai yi amfani da ita wajen neman abin dogaro da kai. Itama Fatima Yahaya ta gode wa shugabannin Shafa’u Rahma bisa shirya horon da kuma kokarin bunkasa rayuwar matasa.
Taron wanda shine na farko, da aka samu nasarar yaye dalibai kimanin 15, ya samu halartar mutane da dama