01/10/2026
JAWABIN CIKAR NIGERIA SHEKARU 66
Daga: Jagoran Kungiyar JIBWIS Nigeria, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau
Bismillahir Rahmanir Rahim.
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.
'Yan uwa Musulmi, 'yan uwa 'yan kasa baki daya.
A yau, Nigeria ta cika shekaru 66 da samun 'yancin kai. Shekaru 66 na tarihi, na darussa, na kalubale, da kuma ni'imomi marasa adadi da Allah Ya yi mana a wannan kasa tamu. Wannan rana ba rana ce ta biki kawai ba, rana ce ta yin tunani da kuma muhasaba.
A wannan rana mai muhimmanci, ina so in gabatar da wannan nasiha da jan hankali a gare mu baki daya.
NA DAYA: JAN HANKALI GA SHUGABANNIN MU
Ya ku shugabannin mu, tun daga matakin kasa har zuwa jihohi da kananan hukumomi, ku sani cewa shugabanci amanar Allah ce kuma Allah zai tambaye ku a kansa gobe Kiyama.
Nigeria ba ta da matsalar albarkatu, tana da matsalar shugabanci na gari. Ku ji tsoron Allah a cikin al'amuran da aka danka muku.
Allah Madaukakin Sarki Yana cewa a cikin Al-Qur'ani mai girma:
ุฅูููู ุงูููููู ููุฃูู
ูุฑูููู
ู ุฃูู ุชูุคูุฏูููุง ุงููุฃูู
ูุงููุงุชู ุฅูููููฐ ุฃูููููููุง ููุฅูุฐูุง ุญูููู
ูุชูู
ุจููููู ุงููููุงุณู ุฃูู ุชูุญูููู
ููุง ุจูุงููุนูุฏููู
โLallai Allah Yana umartar ku da ku bayar da amanoni ga masu su, kuma idan kuka yi hukunci a tsakanin mutane, ku yi hukunci da adalci.โ [Suratun Nisaโi: 58]
Shugabanci ba gata ba ne, nauyi ne. Adalci, rikon amana, da tausayawa talakawa shi ne zai fitar da mu daga halin da muke ciki. Ku rike amana ku tsaya wajen kare Addinin Allah, rayuka da dukiyan al umma, ku sanya ido matuka a kan tsaro, ba hasara cikin duk abinda aka kashe don a Samu zaman lafiya.
NA BIYU: JAN HANKALI GA TALAKAWA
Ya ku 'yan uwa talakawa, ku sani cewa gyaran kasa baya farawa daga sama kadai, yana farawa daga kowane gida.
Matsalar tsaro, rashin zaman lafiya, da talaucin da muke ciki, duk suna da alaka da nisantar mu daga Allah da kuma yadda muke mu'amala da juna. Mu gyara halayen mu, mu dena hassada, yaudara, cin amana, da shiga kungiyoyin da suke kawo fitina.
Allah Ta'ala Yana cewa:
ุฅูููู ุงูููููู ููุง ููุบููููุฑู ู
ูุง ุจูููููู
ู ุญูุชููููฐ ููุบููููุฑููุง ู
ูุง ุจูุฃููููุณูููู
ู
โLallai Allah ba ya canja halin da wata al'umma take ciki, har sai sun canja abin da ke cikin zukatansu.โ [Suratun Ra'ad: 11]
Idan muna son Allah Ya canja mana wannan hali na tsaro da talauci, to dole mu koma ga Allah, mu tuba, mu yi adalci a tsakanin mu.
BANGAREN TSARO DA TALAUCI
A yau babu abin da yafi damun dan Nigeria kamar matsalar tsaro. Kashe-kashe, garkuwa da mutane, fashi da makami, wannan ba al'adar mu bace. Musulunci ya haramta zubar da jinin da bai halatta ba.
Haka nan talauci ya yi yawa. Matasa da yawa sun rasa aikin yi, suna fadawa halin shaye-shaye da miyagun dabi'u. Ina kira ga gwamnati da masu hannu da shuni, ku taimaka ku samar da sana'o'i. Annabi SAW yace: hannun da ke bayarwa yafi albarka fiye da hannun da ke karba.
ADDU'A TA ZAMAN LAFIYA
A karshe, babu abin da zai gyara mana kasar nan sai addu'a.
Ina kira ga kowa da kowa, Limamai, Malamai, Iyayen kasa, Matasa da Mata, mu dage da addu'a ga Nigeria.
Allah Ya bamu zaman lafiya, Ya kawo mana karshen ta'addanci da tashin hankali.
Ya Allah, Ka ba Nigeria zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya Allah, Ka shiryar da shugabannin mu hanya madaidaiciya.
Ya Allah, Ka wadatar da talakawan mu, Ka yaye mana talauci da yunwa.
Ya Allah, Ka hada kanmu, Ka hana zubar da jinin mu.
Ya Allah, Ka sa Nigeria ta fi yadda take a baya, Ka sanya ta zama kasa mai albarka.
Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum.
Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau
Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) Nigeria
1st October, 2026
Jibwis Nigeria