14/06/2026
KUDIRIN SHUGABAN MAJALISAR WAKILAI TA TARAYYA NA INGANTA HARKAR ILIMI DA MALAMAI
.... Kwalliya ta biya kudin sabulu
Lawal Shehu Aliyu
June 14, 2026
Alhamdulillah, tun daga ranar Juma'a da ta gabata wato Ranar Dimokradiyya ta Ƙasa (June 12, 2026) da mai girma Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya, Rt. Hon Abbas Tajudeen PhD GCON (Iyan Zazzau) ya kaddamar da rabon baburan hawa ga Malaman na Primary da Secondary kashi na biyar tun daga zamowan sa Shugaban Majalisar Wakilai a shekara ta 2023 a inda a wannan karo Malamai Dubu Daya (1000) s**a amfana da wannan rabo.
Wannan rabon kayan Alkhairi da ake yiwa Malaman makarantun lokaci zuwa lokaci wani tsari ne na musamman da Shugaban ya kawo don tausayawa tare da karfafa gwiwa ga Malamai duba da muhimmiyar rawa da suke takawa wajen inganta rayuwar Al'ummah wanda har suke da wani take na cewa "No Teacher No Nation" ma'ana idan fa aka ce babu Malami to ita kanta kasar ma babu ita. Kenan kasa baza ta kasance ba sai da Malamai.
Salon kyautatawa Al'ummah musamman ma Malamai da Shugaban Majalisar Wakilai ke yi tun kafin ma ya zamo Shugaban Majalisa baya rasa nasaba da sanin mahimmancin Ilimi da yayi kasancewar sa tsohon Malamin Makaranta wanda ya fara karantarwa tun a matakin farko wato Primary level har izuwa matakin karshe wato Tertiary level inda ya dakata da harkar koyarwa a matsayin (HOD Accounting) a Jami'ar jihar Kaduna gabanin ya shiga harkar siyasa.
A wani jawabi da Shugaban ya gabatar a shekarar 2023 a ofishin mazaba dake Danmagaji Zaria wato (Constituency Office) ya bayyana aniyar sa na bayar da mahimmanci matuka ga harkar ilimi a inda har ya kudiri aniyar cewa In sha Allahu kafin ya kammala jagorancin nan sai ya samarwa dukkan Malamai da ababen da zasu saukaka masu gudanar da harkokin su na koyarwa. Alhamdulillah, ko a yanzun za'a iya cewa haƙa ta cimma ruwa don izuwa yanzun akwai makarantun da duk Malaman dake ciki an kammala basu babura wasu kuma ana gab da kammalawa. Ga tallafin kayan abin masarufi da shima ake badawa lokaci zuwa lokaci don saukaka rayuwa.
Samar da sabbin manyan makarantu da ake kira da Tertiary Institutions tare da samar da manyan gine-gine a wasu daga cikin tsaffin makarantun, gyaran makarantun Primary da Secondary, samar da tallafi ga dalibai wato Scholarship irin sa na farko a tarihin jihar Kaduna, bayar da tallafin karatu ga daliban gaba da Primary a inda dubban dalibai s**a amfana da tallafin NECO, WAEC da JAMB, daukar nauyin wasu dalilai dake karatu a Malaysia a yanzun haka da duk wasu nau'o'i da zasu tabbatar da kudirin Shugaban Majalisar na inganta bangaren Ilimi kamar yadda ya bayyana tun a farko sun isa su tabbatar cewa tabbas "kwalliya ta biya kudin sabulu" kamar yadda masu iya magana ke cewa.
Mai ya rage a gare mu yanzun, shine Addu'a da goyan baya ga wannan bawan Allah da kullun burin sa shine samar da hanyoyin da zasu saukakawa Al'ummah a fannin rayuwa. Allah ya kara yi masa jagora ya kuma kare shi daga dukkan sharri, Allahumma Ameen 🤲
Iyan Zazzau Alkhairi ne!