TEDxZaria

TEDxZaria TEDxZaria is making history as the first TEDx event in Hausa - a language spoken by over 150 million people across Africa.

‎Mai Jawabi Na Tara‎‎Dr. A. S. Abdurrasheed ƙwararren Injiniyan Gine-gine da Muhalli ne, mai bincike, malami, mai gabata...
18/09/2026

‎Mai Jawabi Na Tara
‎
‎Dr. A. S. Abdurrasheed ƙwararren Injiniyan Gine-gine da Muhalli ne, mai bincike, malami, mai gabatar da jawabai a tarurruka, kuma mai rajin bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire. Ya ƙware ne a fannin ilimin sarrafa ruwa da kimiyyar ruwan ƙasa (Hydraulics and Hydrology). Ya samu digirin digirgir (Ph.D.) a fannin Civil and Environmental Engineering daga Universiti Teknologi PETRONAS (UTP), Malaysia, kuma a halin yanzu yana aiki a matsayin Babban Malami (Senior Lecturer) a Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya.
‎
‎Saboda kishin sa na samar da hanyoyin magance matsalolin injiniyanci mai ɗorewa, bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire, da ƙarfafa matasa a Afirka, Dr. Abdurrasheed yana ƙoƙarin ƙarfafa matasa su ƙirƙiri hanyoyin magance matsalolin da ke damun al'ummomin su, tare da samar da tasiri mai amfani a duniya.
‎
‎Daga cikin nasarorin da ya samu akwai lambar yabo ta Zinariya (Gold Medal Award) a International Invention, Innovation and Technology Exhibition (ITEX), lambar yabo ta Zinariya a Malaysian Technology Expo (MTE), International Award of Merit daga Jamhuriyar Croatia, da kuma Gold Lapel Pin a matsayin Brand Ambassador daga UTP Malaysia.
‎
‎Shi ma mai jawabi ne a TEDx, sannan ya samu Triple Crown Award sau biyu daga Toastmasters International, lambar yabo da ke nuna ƙwarewar sa wajen sadarwa, jagoranci, da ci gaban ƙwarewar aiki. Haka kuma, shi ne wanda ya kafa Zaria Toastmasters Club, inda yake ci gaba da taimakawa wajen bunƙasa iya magana da sadarwa, jagoranci, ƙarfin gwiwa, da ci gaban kai.
‎
‎Baya ga aikin sa na ilimi, Dr. Abdurrasheed ƙwararren mai gabatar da jawabai ne, kuma ya gabatar da manyan jawabai, tarukan horaswa, da bitoci kan ƙirƙire-ƙirƙire, jagoranci, ƙwarewar bincike, ƙirƙirararriyar basira (AI), kasuwanci, da iya magana a bainar jama'a, a cibiyoyi daban-daban a Najeriya da ƙasashen duniya.
‎
‎Babban burin sa shi ne zaburarwa tare da bai wa sabuwar ƙarni na masu ƙirƙire-ƙirƙire, masu bincike, da shugabannin Afirka damar yin tunani mai faɗi, magance matsaloli masu ma'ana, da samar da tasiri mai ɗorewa.
‎
‎Ku sayi tikitin ku na TEDxZaria 2026 domin kasancewa tare da shi a taron.
‎
‎

16/09/2026

Karimat Kasim Aliyu na da saƙo a gare ku!
‎
‎Ranar 17 ga Oktoba, za mu haɗu a Zaria domin sauraron sabbin tunani, hikimomi, labarai da abubuwan da za su sauya rayuwar mu.
‎
‎🎟️ Ku tanadi tikitin ku yanzu: tedxzaria.org.ng
‎
‎

‎Mai Jawabi Na Takwas ‎‎Karimat Qasim Aliyu, wadda aka fi sani da Blind Queen, ƴar shekaru 29 ce wadda aka haifa kuma ta...
14/09/2026

‎Mai Jawabi Na Takwas
‎
‎Karimat Qasim Aliyu, wadda aka fi sani da Blind Queen, ƴar shekaru 29 ce wadda aka haifa kuma ta girma a garin Rigachikun da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna. Mace ce mai jajircewa da juriya, wadda lalurar rashin gani ba ta hana ta gina kan ta da cin ma nasarori a rayuwa ba.
‎
‎Ita ɗin mamba ce a ƙungiyar makafi ta ƙasa wato Nigeria Association of the Blind (NAB) reshen jihar Kaduna. Karimat tana da shaidar karatun malanta ta NCE, inda a lokacin karatun ta ta riƙe matsayin mai kula da asusun sashen karatun ta (Departmental Treasurer).
‎
‎Bayan fannin ilimi, ta taɓa gudanar da aikin koyarwa a makarantar Alfajru Private School, inda ta jagoranci ajin Nursery 1 sannan ta gina dalibai kimanin 25. Haka zalika, ƴar kasuwa ce mai sana'o'in hannu kamar sarrafa abin sha na fruity zoɓo da kuma ƙera kayan kwalliya na sarƙoƙi.
‎
‎Bayanai da gogewar ta sun sanya gidajen talabijin irin su DITV da KSMC TV gudanar da hira da ita domin faɗakar da al'umma da nuna cewa naƙasa ba kasawa ba ce.
‎
‎Tana ci gaba da kasancewa fitila kuma abin koyi ga al'umma, tare da tabbatar da cewa ƙalubalen rayuwa ba shi ne ƙarshen burin mutum ba.
‎
‎Ku sayi tikitin shiga taron TEDxZaria 2026 domin gani da jin abubuwan da take ɗauke da shi.
‎
‎

13/09/2026

‎Mal. Hassan Yakubu na da saƙo a gare ku!
‎
‎Ranar 17 ga Oktoba, za mu haɗu a Zaria domin sauraron sabbin tunani, hikimomi, labarai da abubuwan da za su sauya rayuwar mu.
‎
‎🎟️ Ku tanadi tikitin ku yanzu: tedxzaria.org.ng
‎
‎
‎

‎Mai Jawabi Na Bakwai‎‎Hassan Yakubu ƙwararren masani ne a fannin tallace-tallace da gudanar da harkokin kasuwanci, mai ...
12/09/2026

‎Mai Jawabi Na Bakwai
‎
‎Hassan Yakubu ƙwararren masani ne a fannin tallace-tallace da gudanar da harkokin kasuwanci, mai bada shawara ga ƙananan da matsakaitan ƴan kasuwa (SMEs), sannan malami ne a tsangayar Marketing na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna (Kaduna Polytechnic).

Tare da ƙwarewa mai zurfi a fannoni daban-daban irin su tallace-tallace, rarraba kayan sadarwa, kasuwanci, da bunƙasa tsare-tsaren sana'o'i, yana aiki kafada-da-kafada da masana'antu da ƙungiyoyi domin inganta ayyukan su, ƙarfafa alaka da abokan ciniki, da samun ci gaba mai ɗorewa.
‎
‎Shi ne wanda ya kafa Kada SMEs Hub, cibiyar da ke bai wa ƴan kasuwa horo kan harkokin kasuwanci, jagoranci, haɗin gwiwa da hanyoyin bunƙasa sana'o'in su. Ta wannan cibiyar, ya horas da kuma tallafa wa ƙanana da matsakaitan ƴan kasuwa sama da 3,000 a Arewacin Najeriya.
‎
‎Haka kuma, Malam Hassan shi ne Shugaban Arewa Telecom Operators Agents and SIM Card Dealers Association, inda yake wakiltar wakilan kamfanonin sadarwa da abokan hulɗar kayayyakin data a jihohin Arewa 19 da Abuja.
‎
‎Ku shirya, ku sayi tikitin ku, domin jin abin da zai zo da shi a TEDxZaria 2026.
‎
‎

10/09/2026

‎Dr. Tijjani Ahmad na da saƙo a gare ku!
‎
‎Ranar 17 ga Oktoba, za mu haɗu a Zaria domin sauraron sabbin tunani, hikimomi, labarai da abubuwan da za su sauya rayuwar mu.
‎
‎🎟️ Ku tanadi tikitin ku yanzu: tedxzaria.org.ng
‎
‎
‎

‎Sanarwar Haɗin Gwiwa‎‎Muna farin cikin sanar da ku cewa Waziri (CARES) Foundation ya zama ɗaya daga cikin masu haɗin gw...
09/09/2026

‎Sanarwar Haɗin Gwiwa
‎
‎Muna farin cikin sanar da ku cewa Waziri (CARES) Foundation ya zama ɗaya daga cikin masu haɗin gwiwa na TEDxZaria 2026.
‎
‎Wannan haɗin gwiwar na nuna jajircewar TEDxZaria wajen tallafa wa ƙirƙire-ƙirƙire, fasaha, da yaɗa muhimman saƙonni masu tasiri ga al'umma.
‎
‎Ku kasance tare da mu domin sauraron ra'ayoyi masu canza tunani, musayar ilimi, da tattaunawa tare da mutane masu gina cigaban al'umma.
‎
‎______________________
‎
‎Partnership Announcement
‎
‎We are excited to announce that The Waziri (CARES) Foundation has become one of the official partners of TEDxZaria 2026.
‎
‎This partnership reflects TEDxZaria's commitment to supporting creativity, innovation, and the sharing of impactful ideas that contribute to community development.
‎
‎Join us for an inspiring event featuring thought-provoking ideas, engaging discussions, and opportunities to connect with individuals committed to making a positive difference in society.
‎
‎

‎Mai Jawabi Na Shida‎‎Sa’adatu Yunusa, wadda aka fi sani da Arewa Warrior Queen, mace ce mai jajircewa, juriya, da hange...
09/09/2026

‎Mai Jawabi Na Shida
‎
‎Sa’adatu Yunusa, wadda aka fi sani da Arewa Warrior Queen, mace ce mai jajircewa, juriya, da hangen nesa. Ta yi amfani da gwagwarmayar rayuwar ta wajen gina kan ta da kuma kawo sauyi mai kyau a cikin al'umma.
‎
‎A halin yanzu, ƙwararriya ce a fannin sadarwa tsakanin al'umma (Interpersonal Communication Agent), mai samar da abubuwan ilimantarwa a kafafen sada zumunta (content creator), kuma ƴar kasuwa. Haka zalika, ita Fellow ce a gidauniyar Lead Warrior Academy – Dr. Nasir Sani Gwarzo Fellowship.
‎
‎Sa'adatu tana sadaukar da rayuwar ta wajen wayar da kan jama'a game da cutar sikila (Sickle Cell Disease). Kasancewar ta mai ɗauke da wannan cuta ya koya mata ma'anar haƙuri, juriya, da dogaro da kai, tare da ƙara mata ƙwarin gwiwar amfani da muryar ta wajen faɗakarwa da wayar da kan al'umma.
‎
‎Babban burin ta shi ne ta zamanto jagora mai tasiri wajen dakatar da nuna wariya ga masu ɗauke da cutar sikila, da kuma tabbatar da samun daidaito da shigar da su a cikin al'amura a faɗin Najeriya. Tana alfahari da samun goyon bayan iyali da kuma damar amfanar da al'umma ta hanyar aikin ta.
‎
‎A matsayin ta na Arewa Warrior Queen, tana yin amfani da matsayin ta da labarin rayuwar ta domin barin tasiri mai kyau — tare da burin cewa a ƙarshe za a tuna da ita a matsayin: “Macen da ta kawo sauyi mai ma'ana a rayuwar al'umma.”
‎
‎Ku sayi tikitin ku na shiga taron TEDxZaria 2026 don jin jawabin da take ɗauke da shi.
‎
‎

05/09/2026

Hauwa Shehu na da saƙo a gare ku!

Ranar 17 ga Oktoba, za mu haɗu a Zaria domin sauraron sabbin tunani, hikimomi, labarai da abubuwan da za su sauya rayuwar mu.

🎟️ Ku tanadi tikitin ku yanzu: tedxzaria.org.ng

Address

Zaria

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when TEDxZaria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to TEDxZaria:

Shortcuts

Share