02/04/2026
Assalamu Alaikum;
Kamar yadda sanarwa ta gabata a wannan Gidauniya ta Aitaam 'مؤسسة الأيتام' a tsakanin membobin wannan gidauniya cewa za a dinga gudanar da saukar karatun Alƙur'ani mai girma a duk Larabar ƙarshen wata.
To, Alhamdulillah da yammacin jiya Laraba 1 ga watan Afrilu na shekarar 2026 Miladiyya, daidai da 13 ga watan Shawwal na shekarar 1447 Hijiriyya an gudanar da wannan sauka kamar yadda yake a tsarin tafiyar.
An fara wannan saukar ne da yammacin jiya a muhallin Masallacin Madrasatu Hidayatis-sibyan, inda bayan kammala saukar karatun Alƙur'ani mai girma hizifi Sittin (60), Maulana Sheikh Ahmad Abdul’azeez ya rufe muhallin mai albarka da addu'a, amma ka fin addu'a ya gabatar da kalmomin ƙarfafa ga ita tafiyar ta 'marayu' har yai nuni da ka da a taƙaita ga marayu kawai, akwai du’afa, amma marayu su zama sune 'ahammu' wajen fuskanta, Maulana sun ba da shawarwari mabambanta; Inda daga bisani s**a rufe wannan zama mai albarka da addu'o'insu masu albarka.
Bayan kammala addu'a, an gabatar da ƴar ƙwarya-ƙwaryar walima na godiya ga Allah Ta'ala da neman albarka Alƙur'ani mai girma a tafiyar, bayan an kammala ne aka watse, Alhamdulillah an yi lafiya an tashi lafiya.
Rahoto daga;
Mustapha Muhammad ɗaya daga cikin Media Team na 'Aitaam Foundation' dake Unguwar Jaba ƙaramar hukumar Sabon Garin Zariya.
Ga wasu hotuna da muka ɗauko daga muhallin taron!
Wasalamu Alaikum Warahmatullahi Ta'ala Wabarakatuh.