28/11/2023
ÆŠAN MEDIA.....
Kana Matashi wanda kayi karatu a matakin ND, ko HND, ko NCE, ko Degree, ko har Masters, ko kuma kana so kayi karatun, amma baka da damar yin saboda babu wanda zai É—auki nauyin karatun naka, sannan kuma baka da wata sana'a da kake rufawa kanka asiri da ita. To amma kuma sai kawai kazo kana ta tallata É—an siyasa kusan shekaru 4 zuwa 8, shi kuma É—an siyasar nan ya kasa nema maka aikin yi, ya kasa taimaka maka domin samun ingantaccen ilimi, ya kuma kasa baka isasshen jari wanda za kayi sana'a domin kaima ka rufawa kanka asiri, ka kuma dogara da kan ka ba.
Sallar layya ta gabato sai ya ɗauki ₦10,000 ko ₦20,000 ya baka wai ka sayi Rago,Kuma a hakan ma ba
Ko wane É—an media ne ma yake samun hakan ba, Amma kuma kazo ka ruÉ—e kana ta bambaÉ—anci a social media, da teburin mai shayi kana ta faÉ—ar 8+4, wasu lokutan ma har ana rigima da kai akan shi É—an siyasar, don kawai ka burge shi. To magana ta gaskiya ko kaÉ—an baka san ciwon kanka ba, ya k**ata kuma sake tunani sosai a rayuwar ka, domin nemawa kanka mafita.
Ƴan'uwana matasa Allah (S.W.T) Ya shirye mu, Ya kuma bamu ikon fahimtar abinda shine dai-dai.🤲🤲🤲.!
Signed By: AbdAbdulmalik Jibrin MangahbAbdulmalik Jibrin Mangahngah
28th Nov,2023.