07/08/2022
ENGR. DR. MUTTAQA RABE DARMA SCHOLARSHIP BENEFICIARIES ASSOCIATION
A ranar Juma'a 15 ga watan July 2022, ƙungiyar ɗaliban da s**a samu ɗaukar nauyi da tallafin karatu na Engr. Dr. Muttaqa Rabe Darma sun kai ziyarar gaisuwa ta musamman da godiya a kan ayyukan alkhairi da uban wannan ƙungiya yayi masu wato Engr. Dr. Muttaqa Rabe Darma. Tawagar ziyarar ta samu halartar wasu daga cikin manyan jagorori da kuma membobi na wannan ƙungiya wanda s**a haɗa da Shugaban riƙon ƙwarya wato Rabi'u Ma'aruf, sai mataimakiyar shugaba Rabi'atu Sani Ƙusa, da kuma Sakataren riƙon ƙwarya wato Sulaiman Nasir Sulaiman, sannan kuma akwai jami'in hulɗa da jama'a Imrana Abubakar. Daga cikin sauran membobin ƙungiyar da s**a kai ziyarar, sun haɗa da Usman Ahmed, Amina Mohammed Rimi, Hamisu Mukhtar, Hurairah Abdulmalik, David Jonathan da kuma Umar Maisaje.
Shugaban riƙon na ƙungiyar Rabi'u Ma'aruf shi ne ya fara jawabinsa na godiya, kuma ya bayyana jindaɗin sa akan irin hidima da ɗawainiya da aka yi da su. Jim kaɗan bayan haka, Sakataren ƙungiyar Sulaiman Nasir Sulaiman ya gabatar da ƙudiri tare da manufofin assasa wannan ƙungiya, da kuma buƙatar su na samun amincewa da cikakken goyon baya daga uban wannan ƙungiya.
Hakazalika, ita ma mataimakiyar shugaba Rabi'atu Sani Ƙusa ta tofa albarkacin bakinta, inda ta bayyana farin cikin ta, sannan kuma tayi addu'oi ga shi uban wannan ƙungiya wato Engr. Dr. Muttaqa Rabe Darma. Shi ma Jami'in hulda da jama'a na kungiyar wato Imrana Abubakar ya nuna annashuwarsa akan irin tagomashin da s**a samu lokacin da suke karatu a makarantar Sakandare ta kuɗi ta Mariamoh Ajiri. Sannan shi ma haziƙin ɗalibin nan wato David Jonathan yayi godiya ta musamman tare da nuna farin ciki marar misaltuwa akan kambun kyaututtukan da ya samu sakamakon kasancewa da yayi ɗalibin da yafi kowa hazaƙa a shekarar sa ta farko a makarantar Mariamoh Ajiri. Sauran membobin ƙungiya da s**a halarci taron su ma sun miƙa irin tasu godiyar tare da addu'oi na fatan alkhairi ga uban wannan