14/09/2026
KIRA GA MAHUKUNTA DA AL’UMMA DOMIN CETON RAYUWAR MATASHI ABUBAKAR UMAR (KOLONCY )
Gobir Civic Voice Initiative (GCVI) na kira ga mahukuntan Jamhuriyar Nijar da Najeriya, Sarakunanmu, shugabannin al’umma, da dukkan masu kishin Gobir da jin ƙai, da su taimaka wajen neman mafita ga wani matashi mai suna Abubakar Umar Koloncy, wanda ya shafe kusan shekaru biyu a gidan yari a Jamhuriyar Nijar.
Rahotannin da muka samu sun nuna cewa wannan matashi yana gudanar da sana’ar kabukabu tsakanin iyakar Najeriya da Nijar, a yankin Kwanar Kuya, lokacin da aka k**a shi bisa wani lamari da har yanzu iyalansa da al’ummarsa ke neman cikakken bayani a kansa.
Abin damuwa shi ne, har zuwa yanzu, an shafe dogon lokaci ba tare da samun cikakken bayani kan halin da yake ciki ko kuma yadda za a warware matsalarsa ba.
GCVI na roƙon:
1. Mahukuntan Jamhuriyar Nijar
2. Mahukuntan Najeriya
3. Sarakunan Gobir da shugabannin gargajiya
4. Shugabannin al’umma
5. Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama
Da dukkan masu kishin al’umma
da su taka rawa wajen neman adalci, jinƙai da mafita ga wannan matashi.
Idan akwai wani kuskure ko zargi da ake masa, muna roƙon a bi doka yadda ya k**ata, a tabbatar da haƙƙinsa, sannan a sanar da iyalansa da al’ummarsa halin da yake ciki.
Wannan kira ba wai don tsoma baki cikin aikin shari’a ba ne, kira ne na neman adalci, jinƙai da kare haƙƙin ɗan Adam.
Muna kuma kira ga Sarakunan Gobir, musamman masu ruwa da tsaki a al’ummar Gobir, da su dubi wannan lamari da idon tausayi, domin wannan matashi ɗan al’ummarmu ne, kuma iyalinsa suna buƙatar taimako.
Matashi Abubakar da ne ga martaba sarkin Gobir Ummaru
Don Allah, kada mu yi shiru
Rayuwar ɗan Adam tana da daraja, idan akwai abin da za a iya yi ta hanyar doka, diflomasiyya ko sulhu domin ganin an warware wannan matsala, muna roƙon masu iko da masu ruwa da tsaki su ɗauki mataki.
GCVI