Sawaba Initiative for Humanitarian Development Roni Chapter

  • Home
  • Nigeria
  • Roni
  • Sawaba Initiative for Humanitarian Development Roni Chapter

Sawaba Initiative for Humanitarian Development Roni Chapter This is official account of SAWABA INITIATIVE FOR HUMANITARIAN DEVELOPMENT RONI LG CHAPTER.

Kaji da TsabaWata rana, Fir’auna ya shiga taron majalisar hakimansa riƙe da kaza.Yana matse kazar nan da ƙarfi a ƙarƙash...
12/02/2026

Kaji da Tsaba

Wata rana, Fir’auna ya shiga taron majalisar hakimansa riƙe da kaza.

Yana matse kazar nan da ƙarfi a ƙarƙashin hammatarsa. Yana cikin tafiya, kan ya ƙarasa kan karagar mulki da aka tanadar masa,sai ya fara fizge gashin kazar ɗaya bayan ɗaya. Kazar ta dinga tsala ihu saboda tsananin azabar da ke tattare da wanna izaya ta raahin imani, tana fafutukar ganin ta kuɓuta daga hannun Fir’auna. Amma Fir’auna bai sake ta ba, kuma bai damu da kukan da take yi ba—ya ci gaba da fizge gashin kawai hankalinsa kwance.

Hak8man da ke zauna a majalisar s**a ce masa: “Ya ya ka ke azabtar da wannan ƙaramar dabba haka? Ka sake ta mana.”

Amma Fir’auna bai saurari kowa ba ɗaha cikinsu, sai ma ya ƙara bayar da himma akan wannan ƙeta da ya ke yi.

Daga ƙarshe, bayan ya gama fizge dukkan gashin kazar, sai ya jefar da ita can gefe a ƙasa. Bayan haka nan, sai kuma ya ciro wasu ƴan ƙwayoyin hatsi a cikin wani adiko na alhariri daga aljihun gefen alkyabbarsa ya fara watsawa kazar a ƙasa. A wannan yanayin, kazar tana jin wata irin matsananciyar yunwa, sai ta fara kallon hannun Fir’auna tana dauraron ƙarar zubar tsabar akan ƙarau dake shinfiɗe a fadar.

Fir’auna ya kirata kusa da shi, yana ƙara watsa mata ɗan hatsin. Bayan ɗan lokaci, sai kazar ta zo ta zauna kusa da shi, tana cin waɗannan ƙwayoyin hatsin da ya zubar a ƙasa. Kazar da ta daɗe tana fafutukar tserewa daga hannun Fir’auna, yanzu kuma ta dawo ta zauna kusa da shi—don kawai ƴan ƙwayoyin hatsi da take son tsattsaga.

Duk hakiman da ke majalisar s**a tambaya cike da mamaki: “Mene ne wannan haka ya Shugaban mu?”

Fir’auna ya amsa musu da cewa: “Kamar yaɓda kuka ga kazar nan, to masu zaɓe ma haka suke. Tsawon shekaru huɗu da rabi, muna fige gashinsu da ransu. Sannan a cikin watanni biyar ko shida na ƙarshe, sai mu fara watsa musu ɗan hatsin da bai taka kara ya karya ba. Saboda wannan ɗan hatsin, masu zaɓe su kan mancewa da duk wani zalunci da muka yi musu a cikin shekaru huɗu da rabi—sai su sake zaɓenmu. Don haka za mu v8gaba da yunwatar da su muna figesu da ransu daga bisani idan lokaci ya karatu sai a kuma watsa musu tsaba. Wannan salo ne namu na gwanayen iya tafiyar da talakawa.”

Justice that love gives is a surrender; justice that law gives is a punishment.Long Live SAWABA
04/02/2026

Justice that love gives is a surrender; justice that law gives is a punishment.

Long Live SAWABA

25/01/2026

Hello, good day everyone.

Below is a brief summary of today’s discussion:

Litigation:
Regarding the issue we raised with the Local Government, since there has been no professional or official response, we have decided to file a lawsuit. This case will be taken to a court of law within this week.

Membership:
A Google Form will be created and shared publicly. Interested individuals are encouraged to fill out and submit the form to complete their membership registration.

In conclusion, to those who were unable to attend the meeting, on behalf of SAWABA RNLG Chapter, we sincerely acknowledge and appreciate your efforts and support for this movement. Even though you were not physically present, your spirit and solidarity are with us.

Long Live Nigeria.

Long Live Jigawa.

Long Live RNLG.

Long Live SAWABA.

Aluta continua until
victory is attained.

Sannu, barka da rana kowa da kowa.

Ga takaitaccen bayani kan tattaunawar da muka yi a yau:

1. Shari’a (Litigation):
Dangane da batun da muka gabatar ga Karamar Hukuma, tun da ba mu samu amsa ta hukuma ko ta ƙwarewa ba, mun yanke shawarar shigar da ƙara a gaban kotu. Za a kai wannan shari’a gaban kotu a cikin wannan mako.

2. Membobinci (Membership):
Za a ƙirƙiri Google Form kuma a raba shi ga jama’a. Ana ƙarfafa masu sha’awa su cika fom ɗin su tura domin kammala rajistar membobinsu.

A ƙarshe, ga waɗanda ba su samu damar halartar taron ba, a madadin SAWABA RNLG Chapter, muna godiya ƙwarai da gaske bisa ƙoƙarinku da goyon bayanku ga wannan yunƙuri. Ko da yake ba ku halarta da jiki ba, ruhinku da haɗin kai naku suna tare da mu.

Nigeria ta daɗe.

Jigawa ta daɗe.

RNLG ta daɗe.

SAWABA ta daɗe.

Aluta continua har sai an cimma nasara.

For secretary Usman Alto Roni

Address

Roni Kanhawa
Roni
705104

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sawaba Initiative for Humanitarian Development Roni Chapter posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share