29/07/2026
Gudunmawar mu ga Al'umma
A madadin Shugabancin Rogo First Development Organization (RFDO) tare da abokan aikina na Kwamitin Bunƙasa Ilimi a Ƙaramar Hukumar Rogo, ina farin cikin sanar da al'ummar mu muhimman ayyukan da wannan kwamiti zai sanya a gaba domin bunƙasa ilimi a yankinmu.
Jadawalin Ayyukan Kwamitin:
1. Tattara sunayen manyan masana da malamanmu, kamar Farfesoshi (Professors, PhD holders da sauran ƙwararrun malamai, domin gayyatarsu tattauna da al'umma, su wayar da kan matasa, tare da ba su shawarwari da ƙwarin gwiwa kan ilimi da ci gaban rayuwa.
2. Buɗe ƙofa ga kowa da kowa domin samun cikakken bayanai da shawarwari akan hanyoyin shiga makarantun cikin gida da na ƙasashen waje, tun daga matakin Primary School har zuwa Jami'a (University).
3. Kai ziyara zuwa manyan makarantun sakandare domin ƙarfafa gwiwar ɗaliban da ke shirin kammala karatunsu, tare da zaburar da su kan muhimmancin ci gaba da neman ilimi.
4. Shirya horarwa ta musamman ga malamai a makarantun firamare da sakandare domin inganta hanyoyin koyarwa da amfani da dabarun koyarwa na zamani.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanya albarka a wannan aiki, Ya ba mu ikon cika wannan burin namu cikin nasara.
Haka kuma, muna maraba da duk wata shawara mai amfani daga al'umma domin taimaka mana wajen cimma wannan buri.
English
Repaying Back to the Community
On behalf of the leadership of the Rogo First Development Organization (RFDO) and my colleagues on the Committee on Educational Development, I am pleased to inform the people of Rogo Local Government Area about our key initiatives aimed at promoting educational development in our community.
Our Strategic Priorities;
1. To identify and compile a database of distinguished scholars from Rogo, including Professors, PhD holders, and other accomplished academics, and invite them to engage with the community by mentoring and inspiring our young people while sharing their knowledge and experiences.
2. To establish an open platform where students, parents, and members of the public can receive guidance and counselling on educational opportunities and admission pathways into both local and international institutions, from primary education through university.
3. To organise visits to secondary schools to motivate and encourage graduating students to pursue higher education and strive for academic excellence.
2. To organise professional development training for primary and secondary school teachers, equipping them with modern teaching methods and best educational practices.
We pray that Almighty Allah grants us wisdom, strength, and success in accomplishing this important mission.
We also warmly welcome constructive suggestions and support from members of the community to help us achieve these objectives.
Dr. Abdullahi Nazifi Abdullahi
Chairman, Committee on Educational Development
Rogo First Development Organization (RFDO)