27/08/2026
MSSN NINGI AREA COUNCIL TA KARRAMA HAKIMIN NINGI DA LAMBAR YABO DA GODIYA,
Cikin hukuncin Allah Madaukakin Sarki, yau Alhamis, 27th August, 2026 Ƙungiyar Dalibai Musulman Nijeriya reshen karamar hukumar Ningi ta karrama Mai Girma Hakimin Ningi, Ciroman Ningi, Alh Yusuf Yunusa Danyaya (Allah Ya ja kwana masu albarka) da lambar yabo da godiya bisa jajircewar sa da kuma gagarumar gudummawar da yake bawa wannan kungiya a matsayin sa na Uba, musamman rawar gani da ya taka wajen samun babbar nasarar aiwatar da programs na Quiz and Essay Competitions na Jihar Bauchi wanda ya gabata a cikin garin Ningi sati daya da ya wuce.
MSSN ta gabatar da wannan lambar yabo ne ta hannun zababben Shugaban Karamar Hukumar Ningi, Alh. Yahuza Adamu PhD, Ajiyan Ningi a cikin ofishin sa dake cikin sakateriyar karamar hukumar Ningi. Kamar yadda mai karatu yake gani a cikin hoto, Mai Girma Ciyaman ne yake mikawa Mai Girma Ciroman Ningi lambar yabo a madadin MSSN Ningi Area Council.
Daga karshe, Amir na Kungiyar Dalibai Musulman Nijeriya reshen karamar hukumar Ningi, Muhammad Salis Aliyu ya gabatarwa Ciyaman takardar taya shi murna a bisa samun matsayi na shugaban karamar hukumar Ningi a madadin Kungiyar. Ciyaman ya yi jinjina ga Ciroma kuma ya nuna farin cikin sa bisa wannan dama da MSSN ta ba shi.
MSSN tana godiya ga Ciroman Ningi da kuma Ciyaman na karamar hukumar Ningi da mataimakin sa Hon. Alh. Buhari Alhaji Lawal bisa wannan dama da aka bata. Bayan haka, muna sake gabatar da godiyar mu marar adadi ga dukkan bayin Allah da suke bamu gudummawa domin aiwatar da shirye shiryen mu. Allah Ta'ala Ya sakawa kowa da alkairi. Amin.