13/04/2026
π΄ ππππ’π₯π’π₯ππ‘ ππ-πππ¦ππ‘ (Executive Council)
- WaΙannan fuskoki da muka kawo muku na tsawon kwana goma sha biyu (12), sune Jagororin AL-IHSAN (Executive Members), su ke da hakkin gudanar da duk wani aikin AL-IHSAN da ta taso karkashin Jagorancin Shugaba "Chairman".
- Suna aiki ne da manufa guda 1, wanda shine tabbatar da cewa AL-IHSAN bata kauce daga manufar da aka kafa ta ba, hakan yana faruwa ne da taimakon Allah da kuma shawarwarin jajirtattun Patron da Advisers nasu, zamu kawo muku sunayensu da kuma takaitaccen tarihin su, In Sha Allah.
- Cikin falalar Allah, fiye da kaso 75% na waΙannan Membobi mahaddatan Alqur'ani ne, sannan da yawa daga cikinsu Malaman Addini ne, kuma Ιaliban ilimi ne kwarai da gaske, masu karatu a tafarkin Sunnah, dukkanin su suna da degree a fannin karatun boko, wasu ma sun wuce matakin degree.
- Har ila yau, dukkanin su suna da sana'a da suke yi, wasu Ma'aikatan Gomnatin ne, wasu masu aikin hannu ne haΙe da kasuwanci, kuma kaso mafi yawa (9) daga cikinsu magidanta ne masu iyali, dukkansu kuma matasa ne da basu wuce shekaru 30 ba.
- Alhamdulillah, bama tsarkake kowa a gaban Allah, amma a gaskiya muna kyautatawa waΙannan fuskoki zaton Alkhairi.
- Muna fata Allah ya kara musu Albarka a rayuwan su, ya kara haΙa kawunan su, ya basu daman aikata gaskiya a ko da yaushe, ya kiyaye su daga sharrin masu sharri, Ya kuma saka musu da Gidan Aljannah.
π€ π·ππππππππ πͺππππππππ, π¨π°ππΆπ΄
βοΈ π«ππππ π²ππππ π©πππππ/πΎπππππ¨ππ πππππ:
07060799189 - 09124398473