03/10/2026
Khuduba a kan Shugabanci da tsarin al'umma:
Biyayyar shugaba ba ta kai matsayin biyayyar Allah ba. Idan aka samu sabani, a bin da ya kamata a koma gare shi shi ne Alƙur'ani da Sunnah, tare da bin hanyoyin da s**a dace wajen magance matsalar.
A taƙaice, menene babban saƙon wannan hudubar?
Hudubar tana magana ne akan haƙƙoƙi da nauyin da ke tsakanin shugabanni da jama'a.
JAMA'A:
su girmama shugabanni;
su bi abin da yake na alheri;
su yi nasiha cikin hikima;
su guji zagi, tada zaune tsaye da rikici;
kada su bi umarni idan umarnin ya ƙunshi saɓon Allah.
SHUGABANNI:
su ji tsoron Allah;
su yi adalci;
su kare mutuncin jama'a;
su kiyaye dukiyar jama'a;
kada su zalunci mutane;
kada su fifita attajirai ko 'yan uwa saboda matsayi;
su yi mulki a matsayin amana, ba hanyar bin son zuciya ba, su hana fashi da makami, satar alumma domin biyan kudin fansa da kuma hana cin hanci da rashawa.
BABBAN DARASIN KHUDUBAR:
1. Shugaba ba shi da ikon zaluntar jama'a,
2. kuma jama'a ba su da ikon yin barna da fitina da tada zaune tsaye.
3. Dukansu suna da hakkoki da nauyin da Allah Ya ɗora musu.
4. Idan shugaba ya yi adalci, jama'a s**a yi biyayya cikin abin da ya dace, kuma aka yi nasiha cikin hikima, hakan na taimakawa wajen samun adalci, zaman lafiya, haɗin kai da tsaro a cikin al'umma.
Dr. Muhammad Rabiu Abba
Masjid Abubakar Saddiq. Katsina
18/08/2026