Munazzamatul Fityanul Islam, Nasarawa state

Munazzamatul Fityanul Islam, Nasarawa state FAG Of Young Muslim Congress of Nigeria, Nasarawa State Islamic first Aids Group

14/05/2026

Ku saurara kuji 👇

Sanarwar majalisin zikirin goron Sallah daga zawiyyar Muqaddam kwamandan Agaji jihar Nasarawa Alh Hassan Abdullahi a tud...
19/04/2026

Sanarwar majalisin zikirin goron Sallah daga zawiyyar Muqaddam kwamandan Agaji jihar Nasarawa Alh Hassan Abdullahi a tudun amba, layin police station Lafia, gobe Litinin 20/04/2026.

Labari cikin hotuna:Majalisar agajin Munazzamatul Fityanul Islam, Nasarawa state, karkashin jagorancin Muqaddam Alh. Has...
18/04/2026

Labari cikin hotuna:

Majalisar agajin Munazzamatul Fityanul Islam, Nasarawa state, karkashin jagorancin Muqaddam Alh. Hassan Abdullahi, ta halarci daurin Auren daya daga cikin member ta Mallama Sha'awanatu Badamasi da angon ta Mallam Ayuba Sidi a angwan Ganuwa dake karamar hukumar Keffi Jihar Nasarawa.

Tawagar yan agajin ya haɗa da Kwamandan Rundunar agajin Munazzamatul Fityanul Islam reshen FCT Abuja karkashin jagorancin Mallam Abubakar Rijana da iyayen kungiya ɓangaren Jihar Nasarawa.

Mallama Sha'awanatu Badamasi daya ne daga cikin jajirtattun yan Agaji da Allah ya azurta wannan kungiya da ita.

Mai girma Kwamandan Jihar Nasarawa da sauran manyan baƙi sun yi mata nasiha, jan kunne da addu'o'i a zaman ta na aure da zata fara daga yau.

Allah ya azurta su da hakuri, juriya da zuri'a Nagari alfarma Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama.

Allah yasa kowa ya koma gidan sa lafiya Amin.

YMC MEDIA DIRECTORATE NASARAWA STATE

Muna gayyatar kowa da kowa, Allah ya bada ikon halarta Amin!
16/04/2026

Muna gayyatar kowa da kowa, Allah ya bada ikon halarta Amin!

Labarai Cikin hotuna:PANDA DEVELOPMENT AREA TA GABATAR DA TARON KARSHEN WATAKungiyar Munazzamatul Fityanul Islam reshen ...
15/04/2026

Labarai Cikin hotuna:

PANDA DEVELOPMENT AREA TA GABATAR DA TARON KARSHEN WATA

Kungiyar Munazzamatul Fityanul Islam reshen Panda Development Area Karu LGA Nasarawa state ta gabatar da taron ta na karshen wata a garin Panda Detachment.

Taron wanda aka saba duk karshen wata a sassan yankin rayawa na Panda Development Area, wannan karon ya haÉ—a taron iyayen kungiya da Mauludi Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama.

A wajen taron ne aka zabi sabbin shugabannin iyayen kungiya na yankin kamar haka:

1. Shugaba/Chairman; Mallam Haruna Usman ( Limamin Gitata )

2. Mataimakin shugaba/Chairman; Mallam Ilyasu Muhammad ( Limamin Gidan Biri )

3. Sakataren iyayen kungiya: Mallam Sulaiman Muhammad

4. Murshid; Shehu Mallam Abubakar Kare.

Bayan kammala taron da rana, an gabatar da Mauludi Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama karo na Shida da kungiyar ta saba duk shekara karkashin jagorancin Murshid Shehu Mallam Abubakar Kare.

Ma'ajin Agajin kungiyar Munazzamatul Fityanul Islam, Nasarawa state, sannan P.R.O na iyayen kungiya Alh. Makiyyu Dahiru ya sami halartar taron.

Allah ya bada lada, yasa kowa ya koma gidan sa lafiya alfarma shugaba, Sallallahu alaihi Wasallama.

YMC MEDIA DIRECTORATE NASARAWA STATE.

LABARAI CIKIN HOTUNA:ZIYARAR SABON CHAIRMAN DIN NASARAWA LGASabon shugaban kungiyar Munazzamatul Fityanul Islam na karam...
09/04/2026

LABARAI CIKIN HOTUNA:

ZIYARAR SABON CHAIRMAN DIN NASARAWA LGA

Sabon shugaban kungiyar Munazzamatul Fityanul Islam na karamar hukumar Nasarawa dake jahar Nasarawa Alh. Yakubu Yusuf Sodangi, yakai ziyara domin sada zumunci da girmamawa ga babban limamin garin Nasarawa Mallam Ahmad Danbaba da shugaban Jama'atul Nasrul Islam na karamar hukumar Nasarawa Mallam Ibrahim Nakaka a gidajensu.

A lokacin ziyarar mai girma Chiyaman ya mika sakon wannan kungiya na Munazzamatul Fityanul Islam, Nasarawa state na Barka da Sallah tare da godiya da jinjina gare su domin hidimar addini da suke yi yau da kullum.

Chiyaman ya samu rakiyar yan Agaji daga cikinsu har da kwamandan Agaji na karamar hukumar Nasarawa Kuma Asst. Training officer Na Jahar Nasarawa Comr. Isah Muhammad da sauransu.

YMC MEDIA DIRECTORATE NASARAWA STATE.

LABARAI CIKIN HOTUNA:MUNAZZAMATUL FITYANUL ISLAM TA JAGORANCI SAUKAR ALQUR'ANI Kungiyar agajin farko na addinin musulunc...
09/04/2026

LABARAI CIKIN HOTUNA:

MUNAZZAMATUL FITYANUL ISLAM TA JAGORANCI SAUKAR ALQUR'ANI

Kungiyar agajin farko na addinin musulunci, Munazzamatul Fityanul Islam, Nasarawa state karkashin jagorancin kwamandan jahar, Alh. Hassan Abdullahi ta gabatar da saukar karatun Alqur'ani mai tsarki a karamar hukumar Keffi.

Saukar Alqur'anin anyi shine kamar yadda aka saba duk shekara domin gabatar da addu'o'i ga kungiyar, da kasa baki daya domin wanzuwar zaman lafiya da samun kwanciyar hankali.

A jawabinsa na godiya ga matalarta taron, Alh. Hassan Abdullahi yace wannan aiki yana daya daga cikin ayyukan wannan kungiya tun kafa ta, inda a Wannan jahar karamar hukumar Lafiya ne ta fara inda sauran kananan hukumomi suma suke yin wannan aiki a ƙalla sau daya a shekara.

Alhaji Hassan Abdullahi ya mika godiyar sa amadadin wannan kungiya ga abokin aikinsa babban kwamandan Agaji na Abuja wanda duk motsin jahar Nasarawa dashi ake yi yau da kullum, inda ya nuna jin dadin shi ga wannan abota da nuna halin kulawa da yan uwa daga Abuja suke yi mana a matsayin mu na makwabtan juna abokan alfahari.

Anyi wannan taro ne ranar Lahadi 5/04/2026 a garin Keffi LGA.

YMC MEDIA DIRECTORATE NASARAWA STATE.

Gayyatar taro daga Panda Development Area, Karu LGA Nasarawa state.Wajen taro, garin Panda Detachment, Panda Development...
02/04/2026

Gayyatar taro daga Panda Development Area, Karu LGA Nasarawa state.

Wajen taro, garin Panda Detachment, Panda Development Area, Allah ya bamu ikon halarta Amin.

19/02/2026
19/02/2026

Zakin Faidha

Address

Masallacin Gabas Markudi Road
Lafia

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Munazzamatul Fityanul Islam, Nasarawa state posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share