Kura First Foundation

Kura First Foundation The official page of Kura concern foundation (Kura First)

28/03/2026

Dole mu fito mu yaki shaye shaye a garin mu in ba haka ba wallahi zamuyi danasani

26/03/2026

MUNA CIKIN MAWUYACIN HALI..

Tabbas muna cikin wani hali na tsoro da tashin hankali a wannan gari namu, kuma abun mamaki mun naɗe hannun mu mun zuba ido muna abun da mukaga dama abun ma kamar bai damemu ba.

Ina magana ne akan harkar Daba dakuma sai da miyagun kwayoyi da ake a lunguna da saƙunan wannan gari namu, da mamaki ace gari kamar wannan garin mahaddata Qur'ani garin manoma ace abun da zamu iya magancewa yana neman gagarar mu, kowa yasan al'umma ita take fara daukar nauyin gyaran mutanen ta kafin hukuma.

Bakin t**in mu da bayan garin mu sun zama wajen cinikayya ta miyagun kwayoyi kuma duk mun zuba ido kowa na tsoron magana yanzu a haka zamu zauna? Haka zamu bar yan bayan mu suci gaba da rayuwa? Shin mun musu adalci?

22/03/2026

Barkan mu da sallah tare da fatan kowa ya gama ibadah lafia. Tabbas lokaci yayi da zamu farka don cigaban garin mu.

24/01/2026

Magana ta gaskia in har zamu dinga barin motoci manya suna hawa t**inan nan na Kura wlh zasu lalatashi cikin kankanin lokacin.

11/01/2026

Jinjina da yabo ga hukumar Yan sanda ta Kura bisa namijn kokari da tayi wajen kamo barayin da s**a sace wayar wutar lantarki don su jefa al'umma cikin damuwa.

Wannan yakara nuna mana cewa tabbas yan sandan mu na Kura suna matukar kokari da bibiyar lamuran al'umma, muna yimusu fatan alkhairi da Addu'a Allah ya kara karfin gwiwa

Mu mutanen Kura muna godia gareka bisa cigaban wannan aikin t**i na 5km, gwamna Abba Mun gode, tabbas ka cire zukata da ...
17/12/2025

Mu mutanen Kura muna godia gareka bisa cigaban wannan aikin t**i na 5km, gwamna Abba Mun gode, tabbas ka cire zukata da yawa daga cikin damuwa da kuma tashin hankalin ƙura da kuma fuskantar ambaliyar ruwa.

Mungode Allah ya kara karfin gwiwa

09/12/2025

Meyasa bazamu hada kanmu ba, kullum ko ina suna fatan su zama tsintsiya madaurinki daya, amma mu siyasar ta rushemu. sai yaushe ?

29/11/2025

Tabbas Kura na bukatar kayan agajin gaggawa, wanda idan gobara ta tashi ko wata rashin lafia za'a dau matakin da yadace

19/11/2025

AKWAI ABUN MAMAKI

Yau kusan wata biyu kenan ana fama da matsalar wutar lantarki a Kura dalilin faduwar da falafalai s**ai, cikin wannan lokaci abun mamaki shine yanda aikin yake tafiyar hawainiya, yau idan an fara gobe sai a tsaya.

Idan matsalar tafi karfin karamar hukuma sai su wuce gaba kamar yanda akeyi a magance matsalar, amma barin al'ummar da ake jagoranta a haka wannan abune mara dadi sosai.

Muna kira ga mahukunta su duba su dage akan wannan matsalar don kawo karshenta. Allah ya bada iko

InshaAllah zamu cigba da amfanar da wannan gari namu mai albarkaKuraFirst
07/11/2025

InshaAllah zamu cigba da amfanar da wannan gari namu mai albarka

KuraFirst

22/10/2025

Babban wani abu da yakamata al'umma suyi shine kula da ransu da lafiyar su, tabbas babu abun da zaka iyayi cikin salama da kwanciyar hankali in babu daya daga cikin biyun nan, abubuwan da suke faruwa akan babban t**in Kura tashin hankali da yawa yake.

Ba abun burgewa bane karya doka kuma ba abun jin dadi bane jin cewa kai kafi kowa, yakamata mu tsiratar da rayukan mu wajen bin dokokin tuki.

A madadin wannan gidauniya muna mika sakon godia ga mai girma gwamna Engr Abba Kabir Yusif bisa cika alkawari da yayi lo...
20/10/2025

A madadin wannan gidauniya muna mika sakon godia ga mai girma gwamna Engr Abba Kabir Yusif bisa cika alkawari da yayi lokacin yakin neman zaben sa na 2023 akan koken al'ummar wannan gari na t**in 5km.

Tabbas gwamna yayi dattako yayi namijin kokari matuka wajen cigaba da wannan aiki.

Mun gode..

Address

Kura LGA
Kura

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kura First Foundation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share