Karaba Da'awa Foundation KDF

Karaba Da'awa Foundation KDF Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Karaba Da'awa Foundation KDF, Ikara Street, Karaba city, Kubau.

🌙 GAYYATA ZUWA MUHIMMIN SHIRI NA ILIMI 🌙Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa BarakatuhMuna farin cikin gayyatar ku zuwa w...
22/03/2026

🌙 GAYYATA ZUWA MUHIMMIN SHIRI NA ILIMI 🌙

Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuh

Muna farin cikin gayyatar ku zuwa wani shiri na musamman mai taken:

“GYARA KAYANKA”

Shiri ne da aka tsara domin karantar da al’umma muhimman abubuwan da s**a shafi ibadu, tun daga tsarki (ṭahāra) har zuwa yadda ake gudanar da ibadu cikin sauƙi da inganci.

📍 Wuri: Babban Masallacin Jumu’ah na Abdurrahman bn Auf, Karaba – Kubau LGA, Kaduna State
📅 Lokaci: Tsawon kwanaki bakwai (7) in shā Allah

🎙 Mai Gabatarwa:
Ibrahim Dahiru Abu-Mukhtar

Wannan dama ce ga:

- Wanda bai san yadda ake ibada ba
- Ko mai son ƙara fahimta da inganta ibadarsa

📖 Annabi (S.A.W) ya ce:
“Neman ilimin addini wajibi ne akan kowane musulmi.”

📡 Ga waɗanda ba za su samu damar halarta ba, za su iya bibiya ta yanar gizo:

Facebook: KARABA DA’AWA FOUNDATION (KDF)
📞 09038719608

Kada ka bari wannan dama ta wuce ka!

"KARABA DA'AWA FOUNDATION(Karaba, Kano State)🌙 TAFSEERIN RAMADAN 2026 (1447AH) 🌙"Watan Ramadan ne wanda aka saukar da Al...
20/02/2026

"KARABA DA'AWA FOUNDATION
(Karaba, Kano State)

🌙 TAFSEERIN RAMADAN 2026 (1447AH) 🌙

"Watan Ramadan ne wanda aka saukar da Al-Qur’ani a cikinsa, shiriya ce ga mutane…"
— Suratul Baqarah: 185

📖 Ku zo mu zauna mu yi nazarin Al-Qur’ani,
mu fahimci saƙonninsa,
mu gyara rayuwarmu bisa koyarwar sa.

🎙 Mai Gabatarwa:
Ibrahim Dahiru (Abu-Mukhtar)

🕌 Wuri: Masallacin Abdurrahman bn ‘Auf, Karaba
🕝 Lokaci: 2:30 PM (Kullum a watan Ramadan)
📅 Shekara: 2026 / 1447AH

✨ Kada ku bari a baku labari.
Ku halarta tare da iyalai da abokai domin samun falalar watan Ramadan."

https://facebook.com/groups/2149295482033485/

Gayyata!!!
15/07/2025

Gayyata!!!

❕
19/06/2025

Allah ya saka da Alkhairi Ibrahim Disina(Dr.)Yan uwa sai mu lura
19/06/2025

Allah ya saka da Alkhairi Ibrahim Disina
(Dr.)

Yan uwa sai mu lura

05/06/2025

DAN BAIWA
ALHAFIZ ALQASIM UMAR JIBRIL ( HOTORO)

Allah ya nufe ni da Sauraran Bayanin shehun malamin kusan duka
Gaskiya wannan bawan Allah Allah ya masa baiwar hadda da kuma iya bijiro da haddar lokacin da ya so,

TAKAITACCEN SAKONSA

1- Malaman mazhaba sun saba kan samuwar rangwamen zuwa juma'a in ta hadu da idi

2- Mahzabar Imam Ahmad ne kadai s**a yarda da anyi rangwame wa kowa in dai ya je Idi in banda liman da kuma wasu daga cikin mamu domin liman ba zai yi sallah shi kadai ba kuma shi dole ne a kansa kamar yadda Annabi Saw ya ke zuwa kuma tunda juma'ar wajibi ne ga wanda bai samu Idi ba da kuma wadan da s**a zabi zuwa tunda zuwan ya fi falala

3- Mazhabar Imam Ahmad da s**a ce an yi rangwamen to fa rangwamen na zuwa juma'a ne ba Sallah gaba daya ba dan haka dole wanda bai je Juma'a ba ya yi Azahar

4- Ya tabbar da raunin Hadithin Abuhuraira

5-Ya inganta Hadithin Zaidu dan Arqam sabo da jahalar
إياس بن أبي رملة
za ta tashi sabo da ba'a san wani Jarhi a kansa ba, kuma ga ingantawar da manyan malamai su ka yi wa hadithin na sa zai sa jahalar ta gushe

5- Hadithin Ibnu Umar bai inganta ba

6- Hadithin Ibnu Abbas kuskure ne Hadithin Abuhuraira ne da ya gabata a ka yi kuskuren jingina shi wa Ibnu Abbas kamar yadda Ibnu majah ya fada a wata nuskhar ta Sunan

7- Athar din Inbu zubairu wanda ya inganta babu maganar bai yi Azahar ba a ciki

8- Athar din Ibnu Zubair da a ka ce bai yi Azahar ba kuma Ibnu Abbas ya ce Ya dace da Sunnah bai inganta ba

9- Dole ne Wanda ya dauki rangwamen zuwa juma'a to zai yi Azahar saboda:
(a) Allah madaukakin sarki ya wajabta sallah biyar a kowacce rana kamar yadda ya ce:
أقم الصلوة لدلوك الشمس إلى غسق الليل الخ
Ku tsayar da sallah sabo da karkatar rana.......
Wadda sallar farko a karkatar rana ita ce Azahar,
Dan haka kullum an umarce mu da yin sallah biyar
Ba zai yuwu a ce sallah hudu ce ta wajaba a ranar idi da ta hadu da Juma'a ba sai da dalili karara da ya rage sallar wunin ta koma hudu
..

05/06/2025

HATTARA DAI....

Ranar Arfa
Ba ranar gyaran gida ba ce, ba ranar yawon kasuwa ba ce, ba ranar bacci ba ce, ba kuma ranar sharholiya ba ce.

Rana ce da Allah ya girmama ta, ya ɗaukaka sha'aninta, ranar da Allah Yake alfahari ga mala'iku akan bayinSA da s**a duƙufa wajen ɗa'a gareshi a filin arfa, rana ce ta kankarar zunubbai, rana ce ta ibada da zage dantse wajen addu'a. Manzon Allah S.A.W yana cewa: ((Mafi alkhairin addu'a ita ce addu'ar ranar arfa, kuma mafi alkhairin abinda na faḍa ni da annabawa da s**a gabace ni; la'ilaha ilal Allah, wahdahu laa sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli shai'in ƙadir)).

Yi ƙoƙari wajen ganin duk wani abu da za ka aikata a wannan rana ya zamo ɗa'a ce ga Allah domin neman kusanci gare SHI.

KA TUNA: In da ace kana da wata kadara mai daraja, za ka bata kulawa ne ta musamman dan kar ta salwanta, to kwatankwacin haka wannan rana take a gurin duk wani mai rai, lafiya da imani da Allah YA sa ya risketa!!!
Dan haka ka kula da ita dan kar ta tafi baka ribaceta ba!!

- Zainab Ja'afar Mahmud
31st August 2017.

05/06/2025

Please note that the Du'a of this day is better than any other du'a

And please 🥺🥺
Include me in your good prayers 🙏🙏🙇🏻‍♂️

JazakumuLLahu khairan

May Allah accept all our Du'as
Allahumma Ameen thumma Ameen ya ilaahal 'Alamiin 🤲🤲🤲

Mu taya junanmu da addu'a, don Manzon Allah SAW ya tabbatar mana Mala'iku suna  roƙawa bawa irin abinda ya roƙawa ɗan uw...
05/06/2025

Mu taya junanmu da addu'a, don Manzon Allah SAW ya tabbatar mana Mala'iku suna roƙawa bawa irin abinda ya roƙawa ɗan uwansa. Gata Ranar ARFA ga Mala'iku sunma addu'a. DAƊI KAN DAƊI🥰..

02/06/2025

DUK WANDA CUTA TA DAME SHI YAYI MAGANI TAKI WARKEWA.

Tun kafin ka fara neman maganin ka roki ALLAH. Idan ma ka nemi maganin-maganin baici ba ka roki ALLAH.

Kayi wannan Addu'ar wadda (ANNABI AYYUB)yayi👇

(رَبِّي إِنِّي مَسَّنِي الضُّرُّ وَأَنْتَ أَرْحَمُ الرَّاحِمِينَ)

(RABBI INNI MASSANIYA DURRU WA'ANTA ARHAMURRAHIMIYN)

(Yaa ALLAH cuta ta same ni kai kuma kaine mai rahama.)
__________________________________________________

Karka ce Allah ka saka mun wannan cutar ka war kar dani. Kar kace haka.

Haka zakace. ALLAH cuta ta sakko kai kuma kaine mai yaye ta ALLAH ka yaye mun.

ALLAH talauci ya da meni ALLAH ka rabani dashi. Kar kace ALLAH ka saka mun talauci.ba aiwa ALLAH haka. Kace talauchi yazo da kansa. saboda ALLAH shi baya turo maka sharri shi da kansa.

Idan kaga ALLAH yai maka wani abu kai kajawo kaga kenan kai ka kawo ba ALLAH ne ya kawo maka ba.

Dan ALLAH ku turawa al'umma su amfana.wanda bai saniba ya sani ta sanadin ka. ALLAH zai baka lada.

Irin yada wannan shine ba asarar data ko asarar bata lokaci.kutura kowa ya sani abokan ka.

Addu'ar kowa zai iyayin ta maza da mata. Ku turawa al'umma.

Mallam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum Hafizahullah

Salihi Ahmad Ibrahim ✍️

Salihi Ahmad Ibrahim

03/05/2025

Idan kin samu namiji dake son ki kuma yana da addini da ƙoƙarin neman na kansa, kawai ki yi aure idan ba haka ba zaki iya nadama nan gaba.

UMAR SHEHU ZARIA

03/05/2025

ماذا أقول وقد بُلِيتُ بِ Sonta
وسَقَتْ فُؤادي لَوْعَةً و Dimauta🤔

Address

Ikara Street, Karaba City
Kubau

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Karaba Da'awa Foundation KDF posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share