KIRI YOUTH Development

KIRI YOUTH Development Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from KIRI YOUTH Development, Community Service, Kiri, Taura local government, Kiri.

Jigawa State ACReSAL State Project Coordinator Alongside the Chairman of Kiri Youth Development.
19/08/2026

Jigawa State ACReSAL State Project Coordinator Alongside the Chairman of Kiri Youth Development.

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu.Alhamdulillah, muna farin cikin sanar da daukacin al'ummar KIRI cewa jiya, ...
18/08/2026

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu.

Alhamdulillah, muna farin cikin sanar da daukacin al'ummar KIRI cewa jiya, Litinin, ƙungiyar ACReSAL (Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes) ta zo Ramin Kwaki da ke KIRI, inda s**a gudanar da cikakken bincike da gwaje-gwaje domin duba halin da ramin yake ciki da kuma tantance yadda aikin gyara zai kasance.

A yayin ziyarar, an duba matsalar da idanu, an gudanar da gwaje-gwajen da s**a dace, sannan aka yi wa al'ummar gari bayani cewa, in Allah Ya yarda, za a yi aikin gyara da cike Ramin Kwaki. Wannan babban abin farin ciki ne ga al'ummar KIRI. 🤲

Wannan cigaba da aka samu bai zo da kansa ba. Ya samo asali ne daga jajircewa, dagewa da ƙoƙarin ƙungiyarmu ta KIRI YOUTH DEVELOPMENT (KYD) wajen ganin an jawo hankalin hukumomi da masu ruwa da tsaki kan wannan matsala da ta daɗe tana addabar al'ummar KIRI.

Muna amfani da wannan dama wajen miƙa saƙon godiya na musamman ga:

Hon. Muftahu Sa'adu Kiri
(Technical Adviser on Higher Education to the Executive Governor of Jigawa State)

da kuma

Alhaji Aminu Kiri Mawaki (Ɗan Gwamna)

Saboda irin jagoranci, ƙoƙari da dawainiyar da kuka yi wajen ganin ACReSAL ta zo KIRI domin duba wannan matsala. Babu shakka, kun nuna kishin al'umma kuma kun taimaka wajen ganin an kai wannan magana matakin da muke gani a yau.

Tabbas kun yi ƙoƙari sosai. Allah Ya saka muku da mafificin alheri, Ya biya muku duk wata dawainiya da kuka yi, Ya kuma sa wannan aiki ya kammala cikin nasara. Ameen Ya Allah. 🤲

Muna kuma kira ga daukacin al'ummar KIRI da mu ci gaba da haɗin kai, haƙuri da addu'a har sai mun ga an kammala aikin.

KIRI YOUTH DEVELOPMENT (KYD)
“Haɗin Kai Don Ci gaban KIRI.”

SANARWA TA MUSAMMAN GA AL'UMMAR KIRIAlhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! 🤲A yau, da misalin ƙarfe 1:00 na rana, ...
17/08/2026

SANARWA TA MUSAMMAN GA AL'UMMAR KIRI
Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! 🤲
A yau, da misalin ƙarfe 1:00 na rana, ƙungiyar ACReSAL (Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes) za ta zo garin KIRI domin duba halin da Ramin Kwaki yake ciki, tare da tantance yadda aikin gyara da cike ramin zai kasance.

Wannan ziyara ta biyo bayan ƙoƙarin da ƙungiyarmu ta KIRI YOUTH DEVELOPMENT (KYD) ta ci gaba da yi wajen ganin an jawo hankalin hukumomi da masu ruwa da tsaki kan wannan babbar matsala da ke addabar al'ummar KIRI.
Muna matuƙar godiya ga Allah da Ya sa ƙoƙarinmu ya fara haifar da ɗa mai ido. Masha Allah! 🤲

Saboda haka, muna kira ga daukacin al'ummar KIRI — maza da mata, manya da yara — da su fito su je wajen Ramin Kwaki domin nuna damuwarmu da irin muhimmancin da wannan aiki yake da shi a gare mu.

Kasancewarmu a wajen za ta ƙara tabbatar wa ƙungiyar ACReSAL cewa wannan matsala ta shafi al'umma baki ɗaya, kuma muna buƙatar a fara aikin cikin gaggawa domin dakile ci gaba da zaizayar ƙasa da kuma kare gidaje, filaye da dukiyoyin jama'a.

KIRI, yanzu lokaci ne na haɗa kai.
Mu fito mu nuna damuwarmu.
Mu fito mu nemi mafita.
Mu fito muyi aikin kai da kai don ci gaban garinmu.

Allah Ya sa wannan ziyara ta zama sanadin samun cikakkiyar mafita ga wannan matsala. Allah Ya taimaki KIRI, Ya kawo mana alheri mai ɗorewa. Ameen Ya Allah. 🤲
KIRI YOUTH DEVELOPMENT (KYD)
“Haɗin Kai Don Ci gaban KIRI.”

09/08/2026

📢 KIRA GA MAHUKUNTA: A CETO KIRI DAGA BARAZANAR ZAIZAYAR ƘASA

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu.

Muna yin kira na musamman ga mahukunta da masu ruwa da tsaki a dukkan matakai, da su gaggauta ɗaukar matakin cike da gyaran Ramin Kwaki da ke KIRI, domin dakile barazanar zaizayar ƙasa da ke ci gaba da jefa rayuka, gidaje da filayen jama'a cikin haɗari.

Muna kira ga Gwamnatin Jiha, Gwamnatin Tarayya, hukumomin da abin ya shafa, ƙungiyoyin sa-kai da sauran masu hannu a harkar ci gaban al'umma da su haɗa kai domin ganin an magance wannan matsala cikin gaggawa kafin ta ƙara muni.

Haka kuma, muna tunatar da Sanata Walin Kazaure kan alƙawarin da ya yi na taimakawa wajen gyara wannan matsala. Muna roƙonsa da ya cika wannan alƙawari, ya zo KIRI domin a aiwatar da aikin cikin gaggawa, kafin lokaci ya ƙure kuma matsalar ta ƙara yin muni.

Wannan ba batun siyasa ba ne; batun rayuka, gidaje, filaye da makomar al'umma ne. Muna fatan dukkan waɗanda suke da ikon taimakawa za su ɗauki wannan kira da muhimmanci, domin a ceci KIRI daga wannan barazana.

Allah Ya sa a samu mafita cikin gaggawa. Ya taimaki KIRI, Ya kare rayukan al'ummarmu da dukiyoyinsu. Ameen Ya Allah. 🤲

KIRI YOUTH DEVELOPMENT (KYD)
“Haɗin Kai Don Ci Gaban KIRI.”

09/08/2026
08/08/2026
08/08/2026
🙏 SAƘON GODIYA GA AL'UMMAR KIRIAssalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu.Ƙungiyar KIRI YOUTH DEVELOPMENT (KYD) tana m...
08/08/2026

🙏 SAƘON GODIYA GA AL'UMMAR KIRI

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu.

Ƙungiyar KIRI YOUTH DEVELOPMENT (KYD) tana miƙa saƙon godiya ta musamman ga daukacin al'ummar KIRI da s**a samu damar halartar tattaunawar da muka gudanar jiya, 7 ga Agusta, 2026, tare da gidan rediyon Sawaba FM, domin tattauna matsalar Ramin Kwaki da irin barazanar da yake yi wa al'ummar wannan gari namu mai albarka.

Muna matuƙar godiya da irin yadda kuka nuna damuwa, haɗin kai da goyon baya. Haɗuwarku da kasancewarku a wajen tattaunawar sun ƙara tabbatar da cewa wannan matsala ta shafi al'umma baki ɗaya, kuma muna buƙatar haɗin kanmu domin ganin an kawo mata mafita.

Hakika, mun gode sosai da wannan ƙoƙari da kuka yi. Allah Ya saka muku da alheri, Ya ƙara haɗa kanmu, Ya tabbatar mana da alkhairinsa, Ya kuma sa wannan yunƙuri namu ya zama sanadin samun mafita mai ɗorewa ga al'ummar KIRI.

Allah Ya tabbatar mana da alkhairinsa. Ameen Ya Allah. 🤲

KIRI YOUTH DEVELOPMENT (KYD)
“Haɗin Kai Don Ci Gaban KIRI.”

📢 SANARWA TA MUSAMMANAssalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu, jama'ar KIRI.Ƙungiyar KIRI YOUTH DEVELOPMENT (KYD) ta...
07/08/2026

📢 SANARWA TA MUSAMMAN

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu, jama'ar KIRI.

Ƙungiyar KIRI YOUTH DEVELOPMENT (KYD) tana gayyatar daukacin al'ummar KIRI zuwa Ramin Kwaki a yau bayan Sallar La'asar domin halartar tattaunawa ta musamman tare da wakilan gidan rediyon Sawaba FM.

Za a tattauna kan babbar barazanar da Ramin Kwaki ke yi wa al'ummar KIRI, musamman yadda ake ci gaba da asarar filaye da gidajen jama'a. Wannan matsala ta shafi kowa, kuma lokaci ya yi da za mu haɗa kai domin a ji muryarmu.

Muna roƙon kowa da kowa da ya halarta. Kasancewarku za ta ƙara tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa wannan matsala gaskiya ce kuma tana buƙatar ɗaukar matakin gaggawa.

Allah Ya kawo mana mafita. Ya karkato da hankalin shugabanninmu zuwa wannan matsala domin su magance ta cikin gaggawa. Ameen, Ya Allah.

Yanzu wannan ita ce babbar matsalar da take addabar jama'ar garin KIRI ya Allah ka kawomana mafita.
25/07/2026

Yanzu wannan ita ce babbar matsalar da take addabar jama'ar garin KIRI ya Allah ka kawomana mafita.

Address

Kiri, Taura Local Government
Kiri

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when KIRI YOUTH Development posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share