26/05/2026
Lajnatul Hisba Ta Ƙara wa Jami’anta Kusan 30 Girma a Katsina
Shugaban Hisba Ya Tunatar da Falalar Azumin Ranar Arfah, haka kuma, Ƙungiyar Lajnatul Hisba Association Of Nigeria reshen jihar Katsina ta gudanar da wani gagarumin taro na ƙara wa jami’anta girma, inda aka ɗaukaka kusan jami’ai 30 zuwa manyan muƙamai daban-daban domin ƙarfafa ayyukan hukumar a faɗin jihar.
An gudanar da taron ne ranar Litinin 25 ga watan Mayu 2026 a Masallacin Khandahar da ke cikin birnin Katsina, tare da halartar ɗimbin jama’a da s**a haura mutum 250, ciki har da malamai, shugabannin al’umma, jami’an Hisba da sauran masu ruwa da tsaki.
Shugaban Lajnatul Hisba Association Of Nigeria reshen karamar Hukumar Katsina, DC. Malam Kabir Muhammad Jihadi (Abu Sudais), wanda ya jagoranci taron, ya bayyana cewa ƙara wa jami’an girma na daga cikin hanyoyin ƙarfafa musu guiwa domin su ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, riƙon amana da kishin addini.
Ya ce ƙungiyar Hisba na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan al’umma kan kyawawan ɗabi’u, tabbatar da zaman lafiya, da kuma yaƙi da munanan dabi’u a tsakanin matasa da sauran jama’a.
A jawabin nasa, Malam Kabir Muhammad Jihadi ya yi kira ga al’umma musamman matasa da su kasance masu kishin ƙasa da addini, tare da tabbatar da cewa sun zaɓi shugabanni nagari a zaɓen shekarar 2027.
“Ya kamata al’umma su zaɓi mutanen kirki masu gaskiya da riƙon amana, waɗanda za su yi aiki domin cigaban jama’a da ƙasa baki ɗaya,” in ji shi.
Haka kuma, shugaban ya yi kira ga musulmai da su yi amfani da kwanakin ibada wajen neman kusanci ga Allah, musamman ta hanyar azumin ranar Arfah, wanda ya ce yana daga cikin ibadun da ke da falala mai yawa a addinin Musulunci.
Ya tunatar da mahalarta taron muhimmancin haɗin kai da zaman lafiya tsakanin al’umma, yana mai jaddada cewa cigaban kowace al’umma ba zai samu ba sai da haɗin kai da biyayya ga dokoki da koyarwar addini.
Taron ya gudana cikin lumana da nasara, inda mahalarta s**a bayyana jin daɗinsu da irin yadda ƙungiyar Hisba ke ƙoƙarin bunƙasa ayyukanta a jihar Katsina.