KUDU ll Development Forum -KDF

KUDU ll Development Forum -KDF Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from KUDU ll Development Forum -KDF, Community Center, Kofar Kaura Katsina, Katsina.

ZIYARAR KUDU 2 DEVELOPMENT FORUM GA SHUGABAN JAM’IYYAR APC NA KARAMAR HUKUMAR KATSINA KAN MUHIMMAN AIYUKAN CI GABAShuwag...
17/11/2025

ZIYARAR KUDU 2 DEVELOPMENT FORUM GA SHUGABAN JAM’IYYAR APC NA KARAMAR HUKUMAR KATSINA KAN MUHIMMAN AIYUKAN CI GABA

Shuwagabannin Kudu 2 Development Forum sun gudanar da muhimmiyar ganawa da Shugaban APC na Karamar Hukumar Katsina domin tattauna mahimman ayyukan ci gaban al’umma da Forum ɗin ya tsara domin bunƙasa yankinmu.

A yayin taron, Forum ɗin ya mika Takardar Yarjejeniya (MoU) wacce ke ƙunshe da ka’idoji, sharudda, da tsare-tsaren hadin gwiwa domin tabbatar da cikakken aiwatar da ayyukan cikin tsari da gaskiya. MoU ɗin ya yi nufin ƙarfafa haɗin kai, tabbatar da bin doka, tare da tabbatar da cewa kowane aiki ya amfanar da al’ummar yankinmu na Kudu 2.

Shugaban APC na karamar hukumar Katsina ya yaba da hangen nesa da tsare-tsaren Forum ɗin tare da jinjina ga haziqan matasan da s**a assasa wannan tafiyar allhairi, da bayyana goyon bayan jam’iyyar kashi dari bisa dari wajen duk wani aiki da zai inganta rayuwar al’ummar yankin.

Wannan ganawar na nuna wani babban matakin cigaba wajen cimma burinmu na ƙarfafa haɗin kai, inganta ci gaba da samar da dawwamammiyar cigaba ga Kudu 2.

Kudu 2 Development Forum karkashin jagorancin Alhaji Musa Shuaibu ALLE BROSS shirye take wajen inganta Haɗin kai, ci gaba, da gina makoma mai haske musamman bangaren ilimi, sana’o’i da kuma inganta muhalli.

Allah ya ja zamanin KUDU II
Allah ya ja zamanin karamar hukumar Katsina
Allah ya ja zamanin Jihar Katsina da Nijeriya baki daya.

TM Habib Abdulhamid
Media & Publicity
KDF

Address

Kofar Kaura Katsina
Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when KUDU ll Development Forum -KDF posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share