Alkauthar Islamic Foundation

Alkauthar Islamic Foundation Awareness is our Aim

07/07/2026

Copied: Mahmud Galadanci II

Don Allah kalli takalmin Sayyid Ayatollah. Takalmi a ragargaje. Amma a haka shi ne yafi kowa karfin fada a ji a kasa kamar Irann.

Inventory na abunda bawan Allahn nan ya bari gado babu wani abu a cikinsa. Wai karamar pick up truck ce guda daya fa ya bari.

Wannan fa shi ne shugabanci. Shi ne shugaba. Shi ne jagora abun koyi. Da irinsu ke mulkar duniya me kuke tsammanin zai faru? Ai da an samu law, order and justice. Wannan ko shakka babu!

Amma ban yi mamaki ba. Na kalli tsohon video na lokacin da majalisar zartarwar Irann ta zabi Sayyid Ayatollah a matsayin supreme leader a wancan lokacin. Kuka ya saka a kan kawai an zabe shi a matsayin shugaba. Ya Allah 😭.

Tsayawa yayi yana kalubalantar majalisar akan shi bai cancanta ba, akwai wadanda s**a fishi cancanta, su ya kamata a zaba ba shi ba. Shugaban majalisar ya ce duk wanda yake goyon bayan zabar Sayyid Ayatollah ya mike, kowa ya tashi yayi mubayi'a. Kawai sai ya saka kuka.

Wasu suna kashe dukiyarsu don su samu mulki, shi ana bashi karfin iko yana juyarwa. An zabe shi yana kalubalantar zaben. Wasu suna kwadayin shugabanci don azurta kansu, shi bai nema ba, an bashi kuma yaki azurta kan nasa.

Wane irin mutum ne wannan. Ya Allah, ina kaunar bawan nan naka, Sayyid Ayatollah Ali Khamenei. Ina kaunarsa. Bani da shakka akan lallai jinin Imam Ali ne na hakika. Lallai ya yi rayuwa irin ta Imam Ali.

Allah... Ya Allah!

06/07/2026
25/06/2026

اَعْظَمَ اللهُ اُجُوْرَنَا وَاُجُوْرَكُمْ بِمُصَابِنَا بِالْحُسَيْنِ عَلَيْهِ السَّلَامُ وَجَعَلَنَا وَاِيَّاكُمْ مِنَ الطَّالِبِيْنَ بِثَارِهِ مَعَ وَلِيِّهِ الْاِمَامِ الْمَهْدِىِّ مِنْ اٰلِ مُحَمَّدٍ عَلَيْهِمُ السَّلَامُ۔

25/06/2026

A MADADIN ALKAUTHAR ISLAMIC FOUNDATION KATSINA, MUNA SANAR DA AL'UMMA CEWA ZA A GABATAR DA KHATAMAR MAKOKIN ASHURA NA WANNAN SHEKARAR 1448/2026.

RANA: YAU ALHAMIS 25/06/2026
LOKACI: KARFE HUDU DA RABI NA MARECE 4:30PM.
WURI: KATSINA VOCATIONAL AND TRAINING CENTER KATSINA. KUSA DA GIDAN LADAN WAFA.

ALLAH YA BADA IKON HALARTA AMIN.

SIGN........PRO 1
FOR CHAIRMAN.

25/06/2026
Majalisin Ashura zama na biyu a ALKAUTHAR ISLAMIC FOUNDATION KATSINA
24/06/2026

Majalisin Ashura zama na biyu a ALKAUTHAR ISLAMIC FOUNDATION KATSINA

Address

Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Alkauthar Islamic Foundation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share